Idan ba a shirya zabe a watan Yuni ba, to APC ta shiga uku, ta lalace inji Jigon Jam’iyya

Idan ba a shirya zabe a watan Yuni ba, to APC ta shiga uku, ta lalace inji Jigon Jam’iyya

- Salihu Lukman ya bukaci ka da ayi wasa da zaben da za ayi a watan Yuni

- Shugaban PGF ya ce idan aka gagara kiran wannan taro, APC ta shiga uku

- Jigon Jamiyyar ya ce tun 2020 rabon da ayi babban taro na jam’iyyar APC

Babban jigo a jam’iyyar APC, Salihu Lukman, ya ce rashin gudanar da babban taron jam’iyya a watan Yuni, zai iya jefa APC a cikin matsala.

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kungiyar PGF na APC, Salihu Lukman, ya na gargadin kwamitin rikon a kan cigaba da zama a kujera.

Jaridar ta ke cewa Salihu Lukman ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya fitar a birnin tarayya Abuja mai taken: “gwajin da ke gaban jam’iyyar APC.”

KU KARANTA: Har yanzu APC ba ta gauraya ba - Ganduje

Lukman ya ce bai kamata shugabannin rikon kwaryan APC su wuce gona da iri ta hanyar kin gudanar da zaben da aka tsara za a yi a shekarar nan ba.

“Gazawar shirya babban gangami a watan Yunin, 2021, zai nuna cewa kwamitin rikon kwarya bai da sha’awar kare nasarorin da jam’iyya za ta iya samu.”

Ya ce: “Babu dalilin da za a tsaya maganar a shirya zaben watan Yuni ko kuma ka da a shirya.”

“Abin da za a yi muhawara a kai su ne abubuwan da za su wakana wajen zaben; shugabannin da za a zaba, yadda za ayi wa dokokin jam’iyyar kwaskwarima.”

KU KARANTA: Hadimin Jonathan ya jagoranci zanga-zangar da aka yi wa Buhari a Ingila

Idan ba a shirya zabe a watan Yuni ba, to APC ta shiga uku, ta lalace inji Jigon Jam’iyya
Shugaban rikon kwaryar Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni
Asali: UGC

Baya ga sukar shirin kin gudanar da babban zabe na kasa a Yunin 2021, Lukman ya ce akwai bukatar wadanda su rika shirya taron jam’iyya a kai-a kai.

Lukman ya bada shawarwari game da yadda ya kamata a gudanar da harkokin jam’iyyar APC, ta yadda za ayi maganin matsalolin da al’umma su ke fuskanta.

Tun taron da aka yi a Disamban 2020, har yanzu kwamitin rikon-kwarya da ke karkashin gwamna Mai Mala Buni bai kira wani babban taro na jam’iyya ba.

Kwanaki kun ji labari cewa 'Diyar Marigayi Janar Sani Abacha, Gumsu Abacha ta auri Gwamnan Yobe, kuma shugaban riko na jam'iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an yi bikin auren Mai Mala Buni da Gumsu Abacha ne a wani gidan Mohammed Abacha da ke babban birnin tarayya, Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng