Atiku Abubakar zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 – Adamu Atiku
Adamu Atiku-Abubakar, ‘dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mahaifinsa zai sake fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ce Alhaji Adamu Atiku-Abubakar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a jihar Adamawa.
A makon da ya gabata ne Adamu Atiku-Abubakar ya shafe shekaru guda a ofis a matsayin kwamsishinan ayyuka a karkashin gwamnatin PDP ta Ahmadu Finitiri.
Da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a shekara guda, Adamu Atiku-Abubakar, ya yi magana game da siyasar Najeriya da kuma zaben 2023.
Ya ce: “Ni a karon kai na, ban ga wani laifin mahaifina ya fito takarar kujerar shugaban kasa ba. A 2023, mahaifina (Atiku Abubakar) zai yi harin kujerar farko a kasar nan.”
Da ya ke bada dalilansa, sai ya ce: “Saboda (Atiku) ya kasance kwararren ‘dan siyasa, mai dabara, uban gida, wanda ya kuma lakanci harkar siyasa na kusan shekaru 40.”
KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa
Atiku Abubakar ya fara shiga harkar siyasa ne a 1992, ya kuma nemi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP, amma bai yi nasarar samun tikitin jam’iyyar ba.
A 1999 ne Alhaji Atiku Abubakar ya zama mataimakin shugaban kasa bayan ya lashe zabe a Adamawa. Kawo yanzu Atiku ya nemi kujerar shugaban kasa har sau biyar.
Kwamishinan ya ce ya karbi mukamin gwamnati ne bayan lokaci mai tsawo, a dalilin shawarar da mahaifinsa ya ba sa na ya tsaya ya san kan aiki kafin ya shiga gwamnati.
Game da shiga takara, Atiku yace: “Ina nan ne domin in yi wa mutane ne aiki; idan aka kira ni a gida aka bukaci in yi takarar Sanata, ban ga wata matsala game da wannan ba.”
A 2023 zai zama Atiku ya shafe shekaru fiye da 30 ana bugawa da shi. Watakila matsalar da ‘dan siyasar zai samu shi ne a lokacin ya kai shekara 76, kuma ya fito daga Arewa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng