Yanzu-Yanzu: Masoya Buhari sunyi tururuwa zuwa Abuja House a Landan

Yanzu-Yanzu: Masoya Buhari sunyi tururuwa zuwa Abuja House a Landan

- Magoya bayan Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari sun yi tattaki zuwa Abuja House inda Buhari ya ke a Landan a yanzu

- Sun tafi masaukin shugaban kasar ne domin nuna goyon bayansu gare shi inda suka tafi dauke da takardu masu rubutun nuna kishin Nigeria

- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu masu adawa da gwamnatin Buhari sun tafi Abuja House yin zanga-zangan cewa Buhari ya koma Nigeria

Masoya Shugaban kasar Nigeria, Muhammadu Buhari a halin yanzu suna can a gidan gwamnatin Nigeria da ke birnin Landan a kasar Birtaniya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun isa gidan da aka fi sani da 'Abuja House' da takardu masu dauke da rubutu kamar 'Tabbas wannan guguwar za ta wuce', 'Allah na son Nigeria' da sauransu da nufin nuna goyon bayansu ga shugaban kasar.

Yanzu-Yanzu: Masoya Buhari sunyi tururuwa zuwa Abuja House a Landan
Yanzu-Yanzu: Masoya Buhari sunyi tururuwa zuwa Abuja House a Landan
Source: Original

DUBA WANNAN: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

Masu adawa da gwamnatin Buhari, wanda Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa jagora sun tafi gaban gidan gwamnatin suna zanga-zanga a baya bayan nan.

Sun bukaci shugaban kasar da suke zargin yana bannatar da kudaden yan Nigeria, ya tattara kayansa ya koma gida nan take.

A halin yanzu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana hutu a Birtaniya inda ya ce zai tafi domin likitocinsa su duba lafiyarsa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Buhari ya baro Nigeria a dai-dai lokacin da kungiyar likitoci na kasar ke daf da shiga yakin aikin yi.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel