Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

- Dubun wani barawo ta cika bayan ya haka rami a bangon coci ya shiga yin sata

- Mazauna unguwar sun ce sun ga lokacin da ya ke haka ramin amma suka zuba masa ido

- Barawon ya makale a ramin bayan ya shiga cocin ya sato kudi, wayar salula da wasu abubuwan

An kama wani da ake zargi da kutse cikin ginin coci da niyyar yin sata bayan ya makale a wani ramin da ya kutsa ya shiga cikin ginin cocin.

Wanda ake zargin mai suna Agyasuo ya kutsa cikin wani cocin Katolika ne da ke Techimantia, Tano South a kasar Ghana, Vanguard ta ruwaito.

Bidiyon Ɓarawa Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata
Bidiyon Ɓarawa Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

An gano cewa wanda ake zargin ya yi amfani da guduma da wani karfe ne wurin bulla rami a katangan cocin ya shiga amma ya makale a yayin fitowa.

Wasu mazauna unguwar sun ga lokacin da ya ke fasa bangon cocin amma suka zuba wa ikon Allah ido. Bayan ya kammala ya shiga ciki ya saci kudin coci da wayoyin salula.

Sai dai wurin fitowa ya makale hakan yasa mazauna unguwar suka sanar da mai kula da cocin bayan sun lura ya dade a makalen.

Mai kula da cocin ya bude kofa ya kama wanda ake zargin a cikin ramin. A yayin da ya ke rokon a ciro shi, mutane sun amshe kudin da ya sace.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi

An kuma ce an kama shi da wata jaka dauke da wayoyin salula, kwamfuta da wasu kayayyakin da ya sace daga cocin.

Ga bidiyon a kasa:

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Source: Legit.ng

Online view pixel