Yanzu-Yanzu: IGP ya umurci CP ya kamo ƴan IPOB da suka kai wa ƴan sanda hari a Imo

Yanzu-Yanzu: IGP ya umurci CP ya kamo ƴan IPOB da suka kai wa ƴan sanda hari a Imo

- Mohammed Adamu, Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria, ya umurci kwamishinan yan sandan jihar Imo ya kamo wadanda suka kaiwa jami'an tsaro hari a jihar

- IGP na yan sandan ya ce yan kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra, wato IPOB ne suka kai harin da nufin su sace makamai a ma'ajiyar yan sandan

- Mohammed Adamu ya kuma bada umurnin aikewa da karin yan sanda na musamman zuwa jihar ta Imo domin inganta tsaro a jihar

Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria, IGP, Mohammed Adamu, ya dora alhakin kai hari ofishin yan sanda na Imo kan kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Daily Trust ta ruwaito.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar yan sanda, CP Frank Mba ya fitar a madadin sufeta janar na yan sandan, ya ce IGP ya umurci kwamishinan yan sandan jihar Imo ya gudanar da sahihin bincike da nufin gano wadanda suka kai harin domin su fuskanci abinda doka ya tanada musu.

Yanzu-Yanzu: IGP ya umurci CP ya kamo yan IPOB da suka kai hari gidan yari a Imo
Yanzu-Yanzu: IGP ya umurci CP ya kamo yan IPOB da suka kai hari gidan yari a Imo
Source: Original

Ya kuma bada umurnin aikewa da yan sanda na musamman zuwa Imo domin karfafa tsaro a jihar.

"Sufeta Janar na Yan sanda, IGP M.A. Adamu, NPM, mni ya bada umurnin tura karin yan sanda na PMF da sauran yan sanda na musamman zuwa Jihar Imo don inganta tsaro a jihar ta kare cigaba da kaiwa jami'an tsaro da wasu kayayyakin gwamnati masu muhimmanci a jihar hari.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

"IGP ya bada wannan umurnin ne bayan harin da aka kai wa jami'an tsaro ciki har da hedkwatar yan sanda na jihar Imo da Hedkwatar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, NCS, a Owerri a safiyar yau Litinin 5 ga watan Afrilun 2021.

"Binciken da aka fara yi ya nuna cewa maharan da suka iso masu yawa dauke da mugan makamai kamar GPMG, AK49, RPGs, da bamabamai na IED, mambobin kungiyar masu neman kafa kasar Biafra ne wato IPOB da Eastern Security Network, ESN, " a cewar sanarwar

Sanarwar ta ce yan sandan da ke aiki sun dakile yunkurin da aka kai na nufin shiga wurin ajiye makamansu domin a sace. Kazalika, babu wani dan sanda da ya rasa ransa illa guda daya da ya samu raunin bindiga a kafadarsa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Bayan Allah-wadai da harin IGP ya bada umurnin tura karin jami'ai domin kare afkuwar hakan a gaba da kuma kare kai hari a wasu yankunan jihar.

Ya ce an kwato daya daga cikin motocin da maharan suka kai harin da shi kuma ana bincike a kansa.

IGP ya ce rundunar tana iya kokarinta don dakile ayyukan bata gari da ke neman kawo wa hadin kan kasar nan cikas da zaman lafiyan yan Nigeria.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel