Dakatarwa: An shimfidawa kamfanin Azman Air ƙa'idoji kafin jiragensa su fara tashi

Dakatarwa: An shimfidawa kamfanin Azman Air ƙa'idoji kafin jiragensa su fara tashi

- Kwamitin binciken NCAA ya bayyana dalilin dakatar da jiragen Azman tare da shimfida musu ka'idoji

- Hukumar NCAA dai ta dakatar da Azman Air saboda karya wasu dokokin aiki da kuma tantance ingancin jiragen kamfanin

- Mai magana da yawun kamfanin Azman ya ce za su cika ka'idojin cikin mako guda don tabbatar da jiragen sun dawo aiki ba da jimawa ba

Hukumar kula da sauka da tashin jiragen sama na kasa (NCAA) ta bayyana dalilan dakatar da jiragen Azman tare da bayyana wasu ka'idoji da za a cika kafin jiragen su dawo aiki, rahoton Daily Trust.

Tuni kamfanin suka fara yunkurin shawo kan matsalolin da aka bayyana da taimakon sashen kula da jirage.

Dakatarwa: Rahoton binciken ƙwa-ƙwaf ya samu Azman Air da saɓa dokoki
Dakatarwa: Rahoton binciken ƙwa-ƙwaf ya samu Azman Air da saɓa dokoki. Credit: @Channelstv
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

NCAA dai ta dakatar da ayyukan Azman Air saboda dalilin rashin inganci.

A wata samfurin dakata da kwamitin bincike na NCAA wanda wakilinmu ya gani ranar Lahadi ta nuna cewa, an dakatar da jirgin ranar 15 ga watan Maris 2021 bisa rashin cika wasu matakan kariya da hukumar ta shimfida.

Rahoton binciken mai shafi 19 na dauke da sa hannun babban daraktan hukumar NCAA Captain Nuhu Musa dauke da kwanan wata 2 ga Afrilu, 2021.

Ana zargin Azman da karya tarin dokoki da suka saba da kundin dokokin hukumar na shekarar 2006.

Amma kamfanin sun ce suna daukar duk wani mataki don shawo kan matsalar.

KU KARANTA: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Bayan sauke shuganban sashen gyare gyare, sun kuma ware bangaren kiyayewa da tabbatar da inganci wanda da a hade suke, kuma suna neman sabon mai kula da sashen kiyayewa.

Mai magana da yawun kamfanin, Mr Nura Aliyu, wanda ya zanta da wakilan Daily Trust daren da ya gabata, ya ce: "mun fara daukar matakai don cika sharuddan."

Ya tabbatar da cewa duk sharuddan da NCAA ta gindaya za a cika su cikin mako guda don tabbatar da cewa jiragen sun dawo aiki ba da jimawa ba.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel