Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi
- Jami'an hukumar NDLEA sun kama wani mutum ɗan ƙasar Chadi da ke sayarwa yan ta'addan kwayoyi
- An kama Adama Uomar Issa ne a garin Taraba ɗauke da miyagun kwayoyi cikin jakuna da takalman Mata
- Shugaban NDLEA, Mohammed Buba Marwa ya yabawa jami'an ta bukaci su cigaba da jajircewa
Jami'an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta kama wani mutum mai shekara 35 ɗan ƙasar Chadi da ke sayar wa ƴan ta'adda miyagun kwayoyi.
An kama wanda ake zargin, Adama Uomar Issa a jihar Taraba ɗauke da miyagun ƙwayoyi daban-daban, TVC ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira
Sanarwar da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin, Adama Uomar Issa, a ranar Laraba, 31 ga watan Maris a Jalingo, jihar Taraba tare da Tramadol mai 225mg da 250mg wanda nauyinsu ya kai 21.70kg. An kuma kwato Exol. 5; 100,050 France CAF da N61,000.
Babafemi ya ce kwamandan NDLEA a jihar Taraba, Suleiman Jadi, ya ce wanda ake zargin yana magana da harsunan Faransanci da Larabci ne kuma ya yi ikirarin cewa zai tafi da haramtattun kayan zuwa Chadi ne kafin aka kama shi a Jalingo.
Ya ce bincike ya nuna cewa shi babban dilalin miyagun kwayoyi ne na Boko Haram.
Babafemi ya ce an ɓoye muggan ƙwayoyin da aka siyo daga Onitsha jihar Anambra a cikin sabbin jakunkunan mata da takalma.
Ga bidiyon a kasa:
KU KARANTA: NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano
A wani labari mai kama da wannan, jami'an NDLEA sun kai samame Warri Street Kaduna inda suka ƙwato hodar koken da heroin da ƙwayoyin rophynol.
Yayin yabawa jami'an hukumar na johohin Taraba da Kaduna, Shugaban NDLEA, Buba Marwa ya bukaci su cigaba da jajircewa har sai an kawo karshen masu safarar miyagun kwayoyi a kasar.
A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.
Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.
Asali: Legit.ng