Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami

Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami

- Pantami ya musanta rahoton cewa ya ce za'a daure wadanda suka ki yi lambar NIN

- A cewarsa, kafar jaridar ta saki bidiyon idan da gaske haka yace

- Bayan tsokacinsa, kafar jaridar ta cire labarin daga shafinta

Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, ya karyata rahoto dake yaduwa cewa yace duk wanda bai da lambar katin zama dan kasa NIN zai ci zaman gidan yari na tsawon shekaru 14.

Pantami ya bayyana cewa ko sau guda bai ambaci hukuncin daurin shekaru 14 ba. Kawai abinda ya fadi shine an kafa hukumar NIMC na tsawon shekaru 14 yanzu.

Hakazalika ya kalubalanci wata kafar jaridar da ta wallafa labarin cewa ta saki bidiyon inda ya fadi hakan.

"Wadannan mumunan fassara ne. Pantami bai ambaci daurin shekaru 14 ba. Amma yace NIMC ta kwashe shekaru 14 da kafa ta, tun 2007. Tun da yan jarida sun shaida jawabin, kamata yayi a saki bidiyon ga mutane su gani," ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

KU KARANTA: Da alamun jirginmu da ya bace a sararin samaniya ya yi hadari, Hukumar NAF

Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami
Karya akayi min, ban ce za'a kulle wanda yaki yin NIN shekaru 14 ba: Dr Isa Pantami
Source: Twitter

A bangare guda, Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 1 ga watan Afrilu, ta bayyana adadin ‘yan Najeriya da suka yi rajistan lambar shaidar zama dan kasa (NIN).

A cewar Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Ali Isa Pantami, akalla ‘yan kasa miliyan 51 ne ke da lambar NIN din su a yanzu.

Pantami ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja a ranar Alhamis.

DUBA NAN: Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel