Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa

Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa

- Wata 'yar Najeriya da aka haifa da kafa daya da rabi ta shiga kafafen sada zumunta don neman taimako

- Matashiyar da ke rokon ta ce yanayin da take ciki ya haifar mata da radadi da rauni saboda ba za ta iya jin dadin rayuwa kamar kowane mutum

- Ta ce tana bukatar ayi mata kafar roba domin ta samu damar sake amfani da kafafuwan nata

Wata budurwa da ke cikin damuwa ta yi kira ga mutane masu kyakkyawar manufa da su kawo mata dauki don ta sami damar gudanar da rayuwar ta.

An haife ta da ƙafafun da ba su cika ba - ƙafafu ɗaya da rabi.

KU KARANTA KUMA: Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa
Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa Hoto: @GeChi
Asali: Twitter

A wani sako da @Embee_bob ya wallafa a madadinta a shafin Twitter, matashiyar ta ce an haife ta ne da wata cuta mai saurin yaduwa ta hanyar haihuwa.

Cutar kan sa gaɓa daya ya zama ya fi ɗayan gajarta saboda halittan bai tashi yadda ya kamata ba a mahaifa.

Matar da ake magana akan ta wacce aka sani da @GeChi__ ta ce tana tunanin za a yanke kafan da ke da gajarta amma tayi farin cikin ji daga bakin likitanta cewa akwai mafita.

Kuma mafitan shine ta samu kafar roba wanda zai ci N850k.

Yayin da take nuna bakin ciki kan yadda halin da take ciki ya hana ta samun aiki sannan kuma ya hana mata ci gaba da karatu, ta roki ‘yan Najeriya da su taimaka mata saboda ta gaji da radadi da raunuka da nakasar ta haifar mata.

@GeCgi__ ta ce tana son komawa ga amfani da kafafuwanta don ta samu aiki sannan ta taimaka wa mahaifiyarta.

Ta ci gaba da wallafa sakamakon hoton gabar da abin ya shafa.

KU KARANTA KUMA: APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

A gefe guda, wani matashi dan shekara 20 ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar Neja kan laifin kisan matarsa kan sabanin da suka samu kan Kunun karin kumallon da tayi masa.

Bayan sabanin da suka samu, Danladiya bugi matarsa, Zulai Lawal, har ta sume. Daga baya ta mutu a asibiti, rahoton TheNation.

Yayinda aka bayyanashi a hedkwatar hukumar yan sandan jihar dake Minna, Danladi ya bayyana cewa bai taba tunanin matarsa za ta mutu sakamakon bugun ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel