Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN

Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN

- Gwamnatin tarayya ta samu ci gaba abin yabawa a kokarinta na samar da rumbun adana bayanai ga Najeriya

- Wannan ya kasance ne yayinda aka yi wa ‘yan kasa miliyan 51 rajistar NIN tun daga lokacin da aka fara ta a shekarar 2020

- Gwamnati ta bayyana cewa an yi wa katin SIM miliyan 189 rijista zuwa yanzu

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 1 ga watan Afrilu, ta bayyana adadin ‘yan Najeriya da suka yi rajistan lambar shaidar zama dan kasa (NIN).

A cewar Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Ali Isa Pantami, akalla ‘yan kasa miliyan 51 ne ke da lambar NIN din su a yanzu, inji rahoton The Cable.

KU KARANTA KUMA: Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN
Yanzu Yanzu: FG ta bada muhimmiyar sanarwa game da rijistar NIN
Asali: Original

Pantami ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na fadar gwamnati a Abuja a ranar Alhamis.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Pantami ya kuma bayyana karara cewa doka ta tilastawa kowa shiga cikin shirin rajistar, kuma rashin bin wannan umarnin na iya jawowa wasu rasa 'yancin asusun bankinsu da kuma ayyukan sadarwa.

Har ila yau hakan na iya jawo yiwuwar zaman gidan yari na kimanin shekaru 14.

Pantami ya ci gaba da bayyana cewa rajistar ta NIN ita ce hanya mafi kyau ta isa ga yawan mutanen kasar.

KU KARANTA KUMA: Budurwa da aka haifa da kafa daya da rabi ta koka, ta ce tana bukatar sabon kafa

Har ila yau, Ministan ya bayyana cewa an yi rijistar SIM miliyan 189 ta hanyar shirin.

A wani labari, mun ji cewa hukumar Jarabawar Shiga Jami'a (JAMB) ta shirya hanyoyin yin rijista don jarabawarta ta UTME na 2021 a ​​ranar 8 ga Afrilu.

Hukumar ta ce tsarin zai gudana har zuwa 15 ga watan Mayu, 2021. JAMB ta kuma bayyana cewa lallai za bukaci lambar shaidar zama dan kasa (NIN) don yin rajista.

A cewar hukumar jarabawar, babu wani karin lokaci da zata yi wajen siyar da fom din UTME ko kuma na masu neman shiga aji biyu kai tsaye wato DE.

Asali: Legit.ng

Online view pixel