Yanzu-yanzu: Da alamun jirginmu da ya bace a sararin samaniya ya yi hadari, Hukumar NAF

Yanzu-yanzu: Da alamun jirginmu da ya bace a sararin samaniya ya yi hadari, Hukumar NAF

- Hukumar NAF ta bada karin bayani kan jirgin yakinta da ya bace a sararin samaniya

- Kakakin hukumar ya ce matuka biyu ke tukin jirgin lokacin da ta bace

Hukumar Sojin saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa jirgin yakinta Alpha Jet (NAF475) da ta bace a sararin samaniya ta yi hadari.

Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da safiyar Juma'a. 2 ga Afrilu, 2021.

Gabkwet ya bayyana cewa akwai matuka biyu cikin jirgin kuma ya bayyana sunayensu matsayin, FL John Abolarinwa da FL Ebiakpo Chapele.

"Rahoton bincike da hukumar NAF ta tattaro ya nuna cewa jirgin NAF475 da ta bace da matuka biyu ranar 31 ga Maris 2021 ta samu hadari," yace.

"Har yanzu ba'a san abinda ya haddasa hadarin ba kuma ba'a san inda matukan suke ba. Sunayensu Flight Lieutenant John Abolarinwa and Flight Lieutenant Ebiakpo Chapele."

"Har yanzu jirgi na nemansu kuma Sojojin kasa na bincikensu. A yanzu dai muna kyautata zaton za'a ganosu kuma a cetosu."

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 5 da suka ce lallai mulki ya koma kudu a 2023

Yanzu-yanzu: Da alamun jirginmu da ya bace a sararin samaniya ya yi hadari, Hukumar NAF
Yanzu-yanzu: Da alamun jirginmu da ya bace a sararin samaniya ya yi hadari, Hukumar NAF
Asali: Facebook

DUBA NAN: An rantsar da Mohamed Bazoum matsayin sabon shugaban jamhurriyar Nijar

Kun ji cewa jirgin yaki na sojin saman Najeriya dake ayyukan yau da kullum a yankin arewacin Najeriya ya bace.

Wannan yana kunshe ne a wata wallafa da kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkweet yayi a shafinsa na Twitter kuma Legit.ng ta gani a daren Laraba, 31 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel