Wata Sabuwa: Mabarata sunyi zanga zangar rashin samun sadaka a Jihar Oyo

Wata Sabuwa: Mabarata sunyi zanga zangar rashin samun sadaka a Jihar Oyo

-Mabarata sun fito zanga zangar rashin samun sadaka daga mutanen gari

-Wannan ya faru ne a jihar Ibadan a ranar Alhamis 1 ga watan Afrilu

-Ana jitar jitar cewa masu kudi na amfani da mabaratan wajen yin tsibbu

Akalla mabarata 250 a jihar Ibadan, ranar Alhamis, suka fito zanga zangar rashin samun sadaka daga jama'ar gari bayan wani jita jitar cewa masu hannu da shuni na amfani da su wajen tsibbu saboda wata manufarsu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A bisa rahoton, mai magana da yawun mabaratan, Imam Abubakar Abdullahi yace, sarkin Hausawa dake Oja'aba, a jihar Ibadan yayi matukar tsanar mutanan shi.

KU KARANTA: Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajistar katin zabe

Wata Sabuwa: Mabarata sunyi zanga zangar rashin samun sadaka a Jihar Oyo
Wata Sabuwa: Mabarata sunyi zanga zangar rashin samun sadaka a Jihar Oyo Source: Twitter
Source: Twitter

KU KARANTA: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira

A cewar Abdullahi: "Rahoton dake yawo na cewa wasu masu hannu da shuni suna amfani da mabarata da wasu nakasassu wurin yin kudi da wasu tsubbu ba gaskiya bane.

"A sanadiyyar hakane yasa mutane suka nesanta kansu daga wadannan bayin Allah.

"Abinda muka sani shine yan kasuwa, masu talla da direbobi suna zuwa wurin mabaratan nan wadanda yawancinsu makafi ne da guragu suyi chanjin kudi.

"Muna so mu wanke kanmu saboda mutane su daina azabtar da mu akan laifukan da bamu da masaniya akai."

A wani labarin, Gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa na ƙasar nan zasu tattauna da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa kan hukuncin da kotu ta yanke na hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗa su da katin ɗan ƙasa (NIN) ba daga ranar 6 ga watan Afrilu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Laraba wata babbar kotun tarayya dake Lagos ta hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗasu da NIN ba a watan Afrilu.

Jami'an ma'aikatar sadarwa da ma'aikatan kamfanonin sadarwa sun tabbatar wa da Punch cewa ana samun cigaba sosai na masu yin NIN da kuma haɗa shi da layukan waya.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel