Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira
- Gwamnonin jihohin Jigawa da Kebbi sun bada tallafin N20m kowannensu ga ƴan kasuwar Katsina
- Kabiru Abdullahi Barkiya, Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya shima ya bada Naira miliyan 20
- Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi godiya sannan ya ce kawo yanzu an samu tallafin N170m ga yan kasuwar jihar
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, da takwararsa na jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a ranar Laraba, sun ziyarci gwamna Aminu Masari domin yi masa jaje da mutanen Katsina bisa gobarar da ta lashe sassan babban kasuwar Katsina.
Gwamnonin biyu sun sanar da cewa kowannensu zai bada tallafin N20m domin rage wa wadanda suka yi asara a gobarar raɗaɗi, su kuma samu jari, rahoton Daily Trust.
DUBA WANNAN: NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano
Sun yi addu'ar Allah mai girma da ɗaukaka ya mayarwa ƴan kasuwan duk abinda suka rasa yayin gobarar ya kuma kare afkuwar hakan a gaba.
Kazalika, Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Kabir Abdullahi Barkiya, ya bada tallafin N20m ga wadanda gobarar kasuwar ta shafa.
Sanatan ya umurci ƴan kasuwar su ɗauki abinda ya faru a matsayin ƙaddara, inda ya kara da cewa babu adadin kudin da zai mayar musu abinda suka rasa ya kuma yi addu'ar Allah ya taimaka musu.
KU KARANTA: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji
A jawabinsa, Gwamna Masari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka nuna damuwarsu game da gobarar, inda ya ce mutane suna ta bada tallafin kudi duk da cewa ba a riga an kafa gidauniyar neman tallafin a hukumance ba.
Gwamna Masari ya ce zuwa ranar Talata, an samu tallafin fiye da N170m daga mutane daban-daban.
A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.
Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.
Asali: Legit.ng