Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajistar katin zabe

Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajistar katin zabe

- Hukumar INEC a Najeriya ta sanar da ranar ci gaba da rajistar zabe a fadin kasar baki daya

- Hukumar a baya ta dakatar da yin rajistar ne tun shekarar 2018 kafin zaben da ya gabata

- Hukumar ta bayyana cewa, ta kammala shirye-shiryen da suka dace don yin rajistar

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da ranar 28 ga watan Yuni don ci gaba da rajistar masu jefa kuri’a gabanin zaben 2023, TheCable ta ruwaito.

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC, ya sanar da ranar ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Ya zuwa shekarar 2018 lokacin da aka dakatar da rajistar, yawan masu jefa kuri’a a Najeriya ya kai miliyan 84, wanda ke nufin 40% cikin 100% na yawan mutanen kasar.

Hukumar a baya ta yi niyyar sake fara aikin a zangon farko na shekarar 2021.

Amma Yakubu ya ce ba a cimma burin ba saboda wasu ayyuka na bullo da sabbin tsare-tsare don tabbatar da yin rijistar ya dace da ka'idojin Korona, fadada damar masu jefa kuri'a a rumfunan zabe da bullo da sabbin kayan aikin rajistar zabe da kuma fasahar zamani.

KU KARANTA: Shehu Sani: Yajin aikin likitoci ba fa na direbobin tanka bane, a dai duba

Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajisatar katin zabe
Hoto: ripplesnigeria.com
Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajisatar katin zabe
Source: UGC

"Farawa daga ranar Litinin 28 ga watan Yuni 2021, aikin rajistar zai fara ne a duk fadin kasar kuma za a ci gaba da aiwatar da shi tsawon shekara har zuwa kashi na uku na shekarar 2022," in ji shi.

“Duk da haka, ana jaddada za a fara da jihar Anambra inda za a samar da wasu cibiyoyi duba da zaben gwamnan da aka riga aka shirya a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba 2021.

“Domin kammala shirye-shiryen zaben gwamnan, za a dakatar da atisayen rajistar jihar na wani lokaci a watan Agusta 2021. Wannan zai bai wa hukumar damar tsaftace bayanan jihar da buga katin zabe na dindindin ga masu rajista.

“Yayin da lokaci ya ci gaba, hukumar za ta samar da cikakkun bayanai kan aikin rajistar musamman kirkiro wasu abubuwa da za su tabbatar da tsaro da rashin damuwa ga masu rajista.

"A yin hakan, zamu shawarci masu ruwa da tsaki. A zahiri ma, na farko a jerin wadannan shawarwarin zai gudana ne bayan hutun Ista.”

Yakubu ya kirayi 'yan Najeriya da suka haura shekaru 18 kuma basu taba rajistar zaben ba da su yi amfani da wannan damar don ganin sun samu yin rajistar.

KU KARANTA: Najeriya da Dubai sun bankado masu turowa 'yan Boko Haram kudade daga waje

A wani labarin, Gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa na ƙasar nan zasu tattauna da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa kan hukuncin da kotu ta yanke na hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗa su da katin ɗan ƙasa (NIN) ba daga ranar 6 ga watan Afrilu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Laraba wata babbar kotun tarayya dake Lagos ta hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗasu da NIN ba a watan Afrilu.

Jami'an ma'aikatar sadarwa da ma'aikatan kamfanonin sadarwa sun tabbatar wa da Punch cewa ana samun cigaba sosai na masu yin NIN da kuma haɗa shi da layukan waya.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel