Pantami, kamfanonin sadarwa zasu yi taro kan hukuncin kotu na dakatar da rufe layukan waya
- Gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa zasu haɗu don tattaunawa kan hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da rufe layukan waya a watan Afrilu
- A ranar Laraba, wata kotu dake zaman ta a jihar Lagos ta yanke hukuncin dakatar da gwamnatin tarayya rufe layukan waya a watan Afrilu
- Lauya mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Ikechukwu Nnamani, ya shigar da ƙara a gaban kotu yana ƙalubalantar shirin FG
Gwamnatin tarayya da kamfanonin sadarwa na ƙasar nan zasu tattauna da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa kan hukuncin da kotu ta yanke na hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗa su da katin ɗan ƙasa (NIN) ba daga ranar 6 ga watan Afrilu.
KARANTA ANAN: 'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar Laraba wata babbar kotun tarayya dake Lagos ta hana gwamnati rufe layukan da ba'a haɗasu da NIN ba a watan Afrilu.
Jami'an ma'aikatar sadarwa da ma'aikatan kamfanonin sadarwa sun tabbatar wa da Punch cewa ana samun cigaba sosai na masu yin NIN da kuma haɗa shi da layukan waya.
Sun kuma ƙara da cewa za'a duba hukuncin da kotu ta yi na hana rufe layukan waya a watan Afrilu.
Za'a yi taro tsakanin ɓangarorin dake da alhaki kan lamarin don duba hukuncin na kotu kafin wa'adin 6 ga watan Afrilu ya cika.
Tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa,, kuma lauyan kare hakkin bil'adama, Monday Ubani, ne ya shigar da ƙara gaban kotu.
Ya nemi kotun da ta hana gwamnati rufe layukan mutane waɗanda ba'a haɗa su da NIN ba a watan Afrilu kamar yadda take shirin yi.
KARANTA ANAN: Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda Bola Tinubu zai marawa baya a zaben 2023
Daga cikin waɗanda ya shigar ƙarar akwai; Alƙalin Alƙalai na ƙasa, hukumar kula da harkokin sadarwa NCC, da kuma ma'aikatar sadarwa wadda Pantami ke jagoranta.
"Waɗannan sune abubuwan da za'a tattauna a taron da za'ayi kafin wa'adin ya cika ranar 6 ga watan Afrilu," a cewar wani ma'aikacin sadarwa wanda ya nemi a ɓoye sunansa.
Ma'aikacin yace, Shugaban ƙungiyar kamfanonin sadarwa, Ikechukwu Nnamani, shi zai yanke lokacin da za'a yi taron nan gaba.
Ya kuma ƙara da cewa, ministan sadarwa, Isa Pantami, shi zai bayyana ma mutane hukuncin da gwamnati ta yanke kan wa'adin 6 ga watan Afrilu bada jimawa ba.
A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya sha alwashin zaƙulo duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi ma Limamin Cocin Katolika
Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne ta bakin sakataren yaɗa labaran sa a ranar Laraba.
Ya kuma yi kira ga al'umnar jihar da su kwantar da hankalinsu kuma su cigaba da baiwa jam'an tsaro goyon baya da sanar dasu duk wani abu da suke zargi don ɗaukar mataki.
Asali: Legit.ng