Ile-Arugbo: Kotu ta dakatar da Gwamnati daga karbe kadarorin da su Saraki su ka ci gado

Ile-Arugbo: Kotu ta dakatar da Gwamnati daga karbe kadarorin da su Saraki su ka ci gado

- Kotu ta hana gwamnatin Kwara taba kadarorin Marigayi Olusola Saraki

- Kwanaki gwamnatin AbdulRazaq AbdulRahman ta karbe wasu filayensa

- Alkali ya ce ka da a taba wadannan fulotai har sai an ga karshen shari’a

Jaridar The Nation ta ce babban kotun tarayya da ke garin Ilorin, jihar Kwara, ya hana gwamnatin jihar Kwara damar karbe gidan Ile-Arugbo.

Alkalin kotun ya kuma haramta wa gwamnatin Kwara karbe wasu filaye uku da Marigayi Dr. Olusola Saraki ya mallaka a lokacin rayuwarsa.

An samu babban kotun da ta yi fatali da karar da Asa Investment Ltd ya shigar, ya na neman a hana gwamnatin Kwara karbe wadannan filaye.

KU KARANTA: Kotu ta kama Lauyan Saraki da laifin kin kare kansa a shari'ar Ile Arugbo

Rahotanni sun bayyana cewa tuni gwamnatin AbdulRazaq AbdulRahman ta fara gine-gine a kan wadannan filayen da ake ta rikici a kansu a kotu.

A shari’a mai lamba KWS/112/2021, kamfanin Asa Investment da wani mutum sun kai karar gwamnatin jihar Kwara da majalisar dokokin jihar.

Alhaji AbdulRazaq AbdulRahman, kwamishinan shari’a, Darektan hukumar sifayo, shugaban ‘yan sanda na kasa su na cikin wadanda aka hada a karar.

An bukaci gwamnati ta dakatar da karbe wadannan kadarori da marigayin ya bar gado, ko a bada kyautarsu, ko kuma a fara yin wani gine-gine a kansu.

Ile-Arugbo: Kotu ta dakatar da Gwamnati daga karbe kadarorin da su Saraki su ka ci gado
Gwamnan Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami'an Gwamnati su na ba Buhari shawarar banza - Shugaban Majalisa

Wadanda su ka shigar da kara a kan wadannan filaye da ke kan titin Ilofa a unguwar Ilorin GRA, sun nemi ka da a taba fulotan har sai an gama sharia’a.

Alkali mai shari’a, Adenike Akinpelu, ya amince da rokon da aka gabatar, ya bada umarni ka da a taba wadannan filaye har zuwa lokacin da aka karkare karar.

A zaman da aka yi a ranar Talata, kotu da dakatar da sauraron karar sai 19 ga watan Afrilu, 2021.

A bara kun ji cewa har sai da ta kai fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shiga rikicin da ake yi a Kwara tsakanin gidan Saraki da gwamna mai-ci.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Kwara ya ruguza wani tsohon gida na Olusola Saraki, mahaifin Dr. Abubakar Bukola Saraki da Gbemisola Saraki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel