Ile Arugbo: Buhari ya tsoma kansa a rigimar AbdulRazaq da Saraki

Ile Arugbo: Buhari ya tsoma kansa a rigimar AbdulRazaq da Saraki

Rahotanni su na zuwa mana daga Jaridar The Nation cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin rikicin da ake yi a Kwara.

Ku na da labari cewa gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ruguza wani tsohon gida na Olusola Saraki wanda ya rasu a 2012.

Marigayi Dr. Olusola Saraki shi ne Mahaifin tsohon gwamna Dr. Abubakar Bukola Saraki wanda ya rike shugaban majalisar dattawa a 2015.

Shugaban Najeriyar ya sa baki ne bayan Ministarsa, Gbemisola Saraki, ta koka game da wannan abu da gwamnan jihar Kwara na APC ya yi.

Rahotanni sun ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna dmauwarsa game da wannan rigima da ake ta faman yi a jihar Kwara tun kwanaki.

KU KARANTA: Majalisar dokoki ta yi magana game da karbe gidan Saraki

Ile Arugbo: Buhari ya tsoma kansa a rigimar AbdulRazaq da Saraki
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ruguza Ile Arugbo
Asali: Facebook

A dalilin haka ne shugaban kasar ya kafa wani kwamiti a boye domin ya binciko masa gaskiyar lamarin da ya auku da gidan Olusola Saraki.

Gwamnatin jihar Kwara ta hakikance a kan cewa ba a bi doka wajen ba Marigayi Olusola Saraki wannan gida shekaru fiye da 40 da su ka wuce ba.

Rahotannin sun ce gwamnan jihar ya san da batun wannan kwamiti da aka kafa, sai dai babu tabbacin ko Bukola Saraki ya samu wannan labari.

Wata Majiyar ta ce, shugaba Buhari ya na kokarin kawo zaman lafiya ne a jihar da kuma jam’iyyar APC ganin gidan Mahaifin Ministarsa aka rusa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel