Ile-Arugbo: Kotu ta kama Lauyan Saraki da laifin kin kare kansa a gaban kuliya

Ile-Arugbo: Kotu ta kama Lauyan Saraki da laifin kin kare kansa a gaban kuliya

A ranar Alhamis, babban kotun jihar Kwara da ke zama a garin Ilorin, ta hukunta dangin Saraki a dalilin kin kare kansu a shari’ar da ake yi.

Gidan Marigayi Olusola Saraki su na shari’a da gwamnatin jihar Kwara a game da mallakar wani katafaren gidan danginsu wanda aka fi sani da Ile-Arugbo.

A dalilin rashin bayyanar Lauyan kamfanin Asa Investment Limited, Akin Onigbinde, a gaban kotu, Alkali Abiodun Adewara, ya ci tarar wadanda su ke kara.

Abiodun Adewara ya bukaci masu ikirarin mallakar wannan gida da aka rusa da su biya N200, 000 ga gwamnan jihar Kwara, da majalisar dokokin jihar.

Haka zalika Alkali mai shari’a ya ce wadanda su ka shigar da karar za su biya N200, 000 ga Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar da ma’aikatar filaye.

Ba a nan wannan tara ta tsaya ba, iyalin Marigayi Saraki za su bada N50, 000 ga hukumar ‘yan sanda. An ci Saraki tarar ne saboda sun ki bada dama a saurari kararsu.

KU KARANTA: Saraki ya yi magana game da ruguza masu gidan gado da aka yi

Ile-Arugbo: Kotu ta kama Lauyan Saraki da laifin kin kare kansa a gaban kuliya
Gidan Mahaifin Saraki da Gwamnati ta ruguza
Asali: UGC

Adebara ya dauki wannan mataki mai tsauri ne ganin cewa Lauyan da ke kare su Saraki watau Akin Onigbinde, ya ki hallarar zaman da aka yi ranar 7 ga watan Agusta.

Da aka koma zaman shari’a jiya, sai aka ji cewa Akin Onigbinde ya aikowa kotu takardar asibiti da ke nuna ba zai samu zuwa ba saboda Likita ya bukaci ya samu hutu.

Lauyan ya shaidawa kotu ya na bukatar ya huta daga ranar 3 zuwa 10 ga watan Agusta. A watan Yuli ma dai Lauyan ya yi ta bada uzuri, bai halarci zaman da aka yi ba.

Babban Lauyan gwamnatin Kwara, Salman Jawondo, wanda ya tsayawa jihar, ya fadawa Alkali cewa da gan-gan wannan Lauyan ya ke batawa kotu lokaci.

Salman Jawondo ya roki Alkali Adebara ya ci Lauyan kamfanin Asa Limited tara ta yadda zai biya duk wadanda ya ke tuhuma N250, 000, a kuma yi fatali da wannan shari’a.

Ko da cewa wannan shi ne ra’ayin Lauyan da ya tsayawa ‘Yan sandan kasar, Alkali bai yi na’am da gaba daya rokon ba, ya ci tarar N200, 000, amma ya daga shari’ar zuwa Satumba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel