Majalisar Najeriya ta koka a kan yadda manyan Gwamnati su ke ‘yaudarar’ Shugaban kasa

Majalisar Najeriya ta koka a kan yadda manyan Gwamnati su ke ‘yaudarar’ Shugaban kasa

- Ahmad Lawan ya zargi manyan Gwamnati da ba Shugaban kasa shawarar banza

- Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana wannan ne wajen wani zaman da aka yi

- Babu Ministan da ya halarci taron da aka kira duk da an aika masu goron gayyata

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya zargi wasu jami’an gwamnati da yaudarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya ce wadannan jami’ai kan hana shugaban kasa sa hannu a wasu daga cikin kudirorin da majalisar tarayya ta yi aiki a kansu.

Daily Trust ta ce, Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana wannan ne a lokacin da kwamitin kiwon lafiya ya shirya wani budadden zama da aka yi a majalisar.

KU KARANTA: Kafin Buhari ya bar Najeriya, ya amince a dauki sakatarorin dindindin

An gudanar da wannan zama ne domin jin ta bakin mutane kan wani kudiri da ‘yan majalisa su ke neman yi wa garambawul da wasu kudirori da aka kawo.

Wadannan kudirori za su bada damar kafa babban asibitin kashi a garin Kuta, da kuma babbar jami’ar kiwon lafiya ta tarayya a garin Suleja, duk a jihar Neja.

Kafin ya kaddamar da taron, Ahmad Lawan ya nemi jin ko Ministocin lafiya; Dr. Osagie Ehanire, da Dr. Olorunmibe Mamora ko wakilan su sun zo wurin.

Ganin babu wani cikin Ministan ko wakilansu da su ka samu zuwa zaman, shugaban majalisar ya ce hakan ya sa shugaban kasa yake watsi da kudirorinsu.

Majalisar Najeriya ta koka a kan yadda manyan Gwamnati su ke ‘yaudarar’ Shugaban kasa
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan
Source: Facebook

KU KARANTA: Kudin da mu ke tatsa ya ragu – Hameed Ali ya kokawa Majalisa

A cewar Ahmad Lawan, wasu jami’an ma’aikatar gwamanatin su na ba shugaban kasa shawarar banza.

Lawan ya ce ba zai dauki lamarin da wasa ba don ya aika wa Ministocin gayyata, ya ce a karshe sai a fada wa shugaban kasa ka da ya sa hannu a kudirorin.

Dazu kun ji cewa ‘yan Majalisar wakilan tarayya ba su goyon bayan gwamnatin tarayya ta batar da Naira Biliyan 600 da sunan gyaran matatar man Fatakwal.

Bangaren marasa rinjaye a majalisar kasar ta bada shawarar ka da shugaba Muhammadu Buhari ya sake ya fitar da wadannan kudi da cewa za a gyara matatar.

Source: Legit

Online view pixel