Rikici ya sake barkewa tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

Rikici ya sake barkewa tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

- Bayan na Shasha, ana tsoron sabon tashin-tashin a jihar Oyo

- Wannan karon jami'an tsaro sun yi gaggawan kwantar da kuran

- Babu labarin asarar rai ko dukiya, a cewar Kakakin hukumar yan sanda

Sabon rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan, jihar Oyo, yayinda hukumar yan sandan jihar Oyo ta bayyana cewa ta kwantar da kura a unguwar Apata.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya bayyanawa BBC cewa babu wani tashin hankali saboda sun kwantar da kuran yanzu.

Fadeyi wanda yace ba'a samu rashin rai saboda shugaban yan sandan yankin ya tura jami'ai da wuri.

Amma a hirar da BBC tayi da al'ummar Hausawan yankin, sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi.

Wasu mutane da suka gudu daga muhallansu sun samu mafaka an unguwar Sabo kuma sun bayyana yadda rikicin ya barke.

Daya daga cikinsu yace, "Yayinda nike bacci kafin Sallar Asuba, na ji mutane suna gudu kan babura. Sai aka fada min rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa. Ina jin harbe-harbe."

"Wani Bahaushe dan babur ne ya buge wata mata Bayarabiya, sai yan uwanta suka damkeshi kuma suka lallasa shi. Haka ya sa Hausawa suka shiga kare nasu. Yanzu haka ina mafaka a Sabo. An harbi mutum uku amma ba'a sani ko sun mutu ba."

Unguwar Apata wata unguwace da Hausawa masu sayar da kayan miya ke zama a Ibadan.

KU KARANTA: Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni

Rikici ya sake barkewa tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo
Rikici ya sake barkewa tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe

A bangare guda, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bai wa 'yan jihar Kano 185 da suke kasuwanci a kasuwar Shasha da take jihar Ibadan N18,500,000 sakamakon ibtila'in da ya fada musu.

Kwamishinan labarai, Alhaji Garba Mohammed ne ya wakilci gwamnatin, inda ya jagoranci raba N100,000 ga kowannensu a ranar Talata a Ibadan.

Sauran wadanda suka yi rabon sun hada da Alhaji Ibrahim Muktar, kwamishinan kasuwanci da Alhaji Sunusi Muhammed, kwamishinan Ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel