Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi

Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi

- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bai wa 'yan Kano 185, N18,500,000 dake kasuwar Shasha ta jihar Ibadan bisa asarar da suka tafka

- Kwamishinan labarai, Garba Mohammed ne ya wakilci gwamnatin jihar wurin bai wa kowannensu N100,000 a ranar Talata a Ibadan

- A cewar Mohammed, gwamna Ganduje ya sa a ziyarci 'yan jihar da suke kasuwanci a can don gwamnati ta san yadda za ta taimakesu

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bai wa 'yan jihar Kano 185 da suke kasuwanci a kasuwar Shasha da take jihar Ibadan N18,500,000 sakamakon ibtila'in da ya fada musu.

Kwamishinan labarai, Alhaji Garba Mohammed ne ya wakilci gwamnatin, inda ya jagoranci raba N100,000 ga kowannensu a ranar Talata a Ibadan.

Sauran wadanda suka yi rabon sun hada da Alhaji Ibrahim Muktar, kwamishinan kasuwanci da Alhaji Sunusi Muhammed, kwamishinan Ilimi, Vangaurd ta wallafa.

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi
Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A cewar Mohammed, gwamnan ya umarcesu da su kai wa 'yan asalin jihar Kano da suke kasuwanci a garin don su san rawar da gwamnati za ta iya taka musu sakamakon asarar da suka tafka.

"Muna da akalla mutane 185 'yan asalin jihar Kano wadanda tsautsayin nan ya afka musu. Kuma mun gama kasafin cewa kowannensu zai samu N100,000.

"Wadanda kuma suka koma Kano za su je su tattauna da gwamnan. Za mu gano su a Kano kuma mu basu kudaden," a cewarsa.

Ya kara da bayyana yadda suka tattauna dasu don sanin matsalolinsu da abubuwan da suka fuskanta, har suka yi alkawarin zama da gwamnan Oyo don kawo karshen wannan lamari.

Kwamishinan ya bayyana takaicinsa akan yadda lamarin ya faru, kuma yayi kira ga hadin kan gwamnoni da kuma jami'an tsaro.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa

A wani labari na daban, tsohon hafsin sojojin kasa na Najeriya, laftanal janar Azubuike Ihejirika mai murabus, ya shiga jam'iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yayi rijistar jam'iyyar a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, ya rike kujerar shugabancin sojin ne daga 2010 zuwa 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sannan ya bayyana kudirin komawa jam'iyyar APC din ne a garinsu na Isuikwuato dake mazabar Abia ta arewa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel