Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe

Shugaba Muhammadu Buhari zai sake zuwa birnin Landan, Kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya bayyana cewa Buhari zai tafi gobe Talata, 30 ga watan Afrilu, 2021.

A cewar Adesina, Buhari za kwashe fiye da mako guda a Landan kuma zai dawo cikin mako na biyu a watan Afrilu.

"Shugaba Buhari zai garzaya Landan, Birtaniya, ranar Talata 30 ga Maris, 2021 domin duba lafiyarsa," Adesina yace.

"Shugaban zai gana da hafsoshin tsaro da safe, sannan ya tafi. Ana kyautata zaton zai dawo cikin mako na biyu a Afrilu, 2021."

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiyarsa gobe
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel