Abin al'ajabi: Hotunan Makaho yana amfani da kyawawan duwatsu wajen kera tasosin saka fure

Abin al'ajabi: Hotunan Makaho yana amfani da kyawawan duwatsu wajen kera tasosin saka fure

-Wasu hotunan wani makaho sun yadu a kafar sada zumuntar Twitter

-A hotunan an hange makahon yana kera tasosin saka furanni

-Kuma yana hakan ne ba tare da taimakon kowa ba

Nakasa ba annoba bace wacce zata kange mutum daga cimma burikanshi na rayuwa ko samun farin ciki a rayuwa, hakan yasa wani makaho daba'a san ko wanene ba yayi amfani da bajintar da Allah yayi mai madadin bara a kan titi.

A Wasu hotuna da wani mai amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter @ADawakee ya wallafa an ga makahon yana kera tasar saka furanni a kan hanya.

Yana amfani da hannayen shi wajen kere tasar da kyawawan duwatsun, makahon ya nuna bajintar shi kamar mai idanu.

KU KARANTA: Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

Abin al'ajabi: Hotunan Makaho yana amfani da kyawawan duwatsu wajen kera tasosin saka fure
Abin al'ajabi: Hotunan Makaho yana amfani da kyawawan duwatsu wajen kera tasosin saka fure Photo Credit: @ADawakee
Source: Twitter

Za'a iya amfani da tasosin furen wurin kawata gida.

Bashi da wani mai taimaka mai wurin kerawa kamar yadda aka gani a cikin hotunan kuma ba'a san musabbabin abinda yasa ya makance ba.

Mutumin wanda aka ga hotunan shi a Twitter an hange shi da guduma a hanunshi sannan da wata doguwar sanda wacce ya jingine kafarshi da ita.

KU KARANTA: Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai

Yan Nigeria da yawa sun jinjina ma wannan makaho akan banjintar sa na neman na kansa madadin bara akan titi yayinda wasu kuma suka mai addu'a.

A wani labarin, wani gajeren bidiyon Aliko Dangote yana jawabi ga wasu ma'aikatansa ya bazu. Kamar yadda ma'abocin amfani da Twitter mai suna Omasoro Ali Ovie ya wallafa, jama'ar duk ma'aikatansa ne na sabon kamfanin takin zamanin da ya bude.

Ya ce an yi ganawar ne yayin da ake gwada samar da takin zamanin karo na farko.

A sanye da takunkumin fuska, ma'aikatan sun nuna jin dadinsu a kan kalaman Dangote inda suka koma ayyukansu kan na'urori masu kwakwalwa dake gabansu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel