Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai

Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai

- Shugaban kamfanin NNPC ya ce dole sai kudin litar mai ya tashi a Najeriya

- ‘Yan kwadago sun ce ba za su yi na’am da karin farashi a wannan marra ba

- Ana fama da matsin tattali, rashin aikin yi da tsada da tashin farashin kaya

Shugaban kamfanin mai na kasa na NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce gwamnati ta na biyan N100n-N120b a matsayin kudin tallafin fetur duk wata.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban na NNPC ya na cewa ba za su iya cigaba da bada tallafi domin gidajen mai su rike farashin lita a N162 ba.

Ya ce: “NNPC kadai ke shigo da fetur. Mu na sayen mai a farashin kasuwa, mu saida a N162. Ya kamata lita ta kai tsakanin N211 da N234 a gidan mai.”

KU KARANTA: Man fetur: Gwamnatin APC ba ta tausayin talakawa - TUC

Wannan yunkuri da gwamnatin tarayya ta ke yi na taba kudin man fetur ba zai yi wa al’umma dadi ba, don haka kungiyoyin kwadago su ka sa damara.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba a wata hira da ya yi, ya ce jama’a ba za su iya karbar wani karin kudi a halin tsadar kaya da rashin aikin yi da ake ciki ba.

Wabba yake cewa baya ga tsadar rayuwa, annobar COVID-19 ta jikkata mutanen Najeriya, sannan ga matsin lambar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasa.

Amma NNPC ta na ganin babu abin da zai hana farashin fetur tashi. Mele Kyari yake cewa idan aka duba za a ga Najeriya ta fi makwabtanta arahar mai.

Akwai kura bayan NNPC ya ce za a koma saida litar man fetur a kan N234 a gidajen mai
Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Nigeria na shirin yin ƙarin kuɗin dakon mai

Masana su na ganin ya kamata gwamnatin tarayya da NNPC su rika yin gaskiya wajen bayyana wa Duniya abin da ake batar wa da sunan tallafin man fetur.

Wasu na ganin a maimakon a rika kashe Naira biliyan 120 duk wata wajen rage tsadar fetur, zai fi kyau ayi amfani da kudin nan a wajen ayyukan more rayuwa.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani bayan wani taro da aka yi a fadar Aso Villa, kun ji cewa Mele Kolo Kyari ya koka da cewa ba za a iya cigaba da tafiya a haka ba.

Injiniya Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa kudin da ake kashe wa wajen tace litar danyen mai, sannan ayi dakonsa zuwa Najeriya ya na tashi ne a kan N234.

Asali: Legit.ng

Online view pixel