Bidiyon Dangote kai tsaye tare da ma'aikatansa yana kara karfafa musu guiwa
- Wani gajeren bidiyo ya nuna lokacin da Aliko Dangote ya samu lokacin jawabi ga ma'aikatansa a sabon kamfaninsa na takin zamani
- Omasoro Ali Ovie, ya wallafa gajeren bidiyon a shafinsa na Twitter inda yace Dangote yana karawa ma'aikatan karfin guiwa
- Jama'a da yawa da suka kalla bidiyon sun ce akwai bukatar biloniyoyin Najeriya su saka hannayen jari domin habaka tattalin arziki kamar Dangote
Wani gajeren bidiyon Aliko Dangote yana jawabi ga wasu ma'aikatansa ya bazu. Kamar yadda ma'abocin amfani da Twitter mai suna Omasoro Ali Ovie ya wallafa, jama'ar duk ma'aikatansa ne na sabon kamfanin takin zamanin da ya bude.
Ya ce an yi ganawar ne yayin da ake gwada samar da takin zamanin karo na farko.
A sanye da takunkumin fuska, ma'aikatan sun nuna jin dadinsu a kan kalaman Dangote inda suka koma ayyukansu kan na'urori masu kwakwalwa dake gabansu.
KU KARANTA: Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce
KU KARANTA: Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce
A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya ja hankulan dubban jama'a da suka kalle shi a Twitter kuma suka dinga jinjinawa Dangote a kan yadda kai tsaye yayi magana da ma'aikatansa.
Ga wasu daga cikin martanin jama'a da legit.ng ta tsinto muku:
@TorToridb yace: "Wannan ne shugabanci. Jama'a suna magana kai tsaye da ma'aikatansu. Babu abinda ya kai wannan bada kwarin guiwa."
@ndubisi2287 yace: "Abinda nake gani a nan sune dama, ina fatan zamu daina shigo da abincin kaji da taki."
@moruf_olatunji tace: "Don Allah su sa shi a farashin da 'yan Najeriya zasu iya siya."
A wani labari na daban, darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan 'yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.
Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.
Kamar yadda yace, wannan al'amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.
Asali: Legit.ng