Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m

Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m

-Rudunar yan sandan jihar kano ta karrama jami'anta biyu kan kin amsar cin hanci

-Hakan ya faru ne yayinda jami'an suke gudanar da aikinsu a hukumar kare hakkin masu siyan kaya

-Mai magana da yawun rundunar yan sandan ne ya bayyana haka ranar juma'a

Rundunar jihar Kano ta karrama wasu jami'anta biyu kan kin amsar miliyan daya wadda aka gabatar masu a matsayin cin hanci.

Kwamishinan yan sandan jihar, Samaila Dikko, yayi kira ga sauran jamian dasu yi koyi da wadannan jami'an biyu.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure

Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m
Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m Source: Twitter
Asali: Twitter

A wani jawabi daga mai magana da yawun bakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ranar juma'a, yace Garba Rabo da Jamilu Buhari suna gudanar da aikinsu ne a hukumar kare hakkin masu siyan kaya a Jihar a yayin da aka gabatar masu da cin hancin, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Yace a yayin da suke kan aikinsu ne suka samu bayanin cewa akwai wasu gurbatattun kaya da suka kai darajar biliyoyin kudi wadanda aka ajiye a dakin ajiyar kaya a cikin garin Kano.

KU KARANTA: Mun fitar da N288bn kudin tallafin Korona, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m
Rundunar yan sanda ta karrama jami'anta kan kin amsar cin hancin N1m Source: Twitter
Asali: Twitter

"Da jin haka sai jami'an biyu suka garzaya dakin ajiyar kayan,inda aka gabatar musu da cin hancin N1m. Sai suka ki amsar cin hancin suka kwace gurbatattun kayan kuma suka damke wanda ake zargin," A cewar Kiyawa

Shima Manajan Darektan hukumar kare hakkin masu siyan kaya, Baffa Dan'agundi, ya yabawa jami'an akan rashin amsar cin hancin.

Dan'agundi yace hukumar ta yanke shawarar karrama jami'an da N1m saboda kyakkyawan halinsu da suka nuna.

Ya kuma yi kira ga mutane da su cigaba da ba jami'ansu goyon baya su kuma rika godewa wadanda suka gudanar da aikinsu cikin aminci.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin ayyukan yi cikin matasan Karkara ya zama babban kalubalen da ke rura wutan matsalar tsaro a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin karban bakuncin kungiyar masu sarrafa taki a Najeriya (FEPSAN), rahoton DailyTrust.

Shugaban kasan yace shekara da shekaru gwamnatocin da suka shude sun mayar da hankulansu kan raya birane maimakon raya Karkara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel