Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure

- Miyagun 'yan bindiga sun kutsa kwatas din ma'aikatan filin jirgin sama dake Jos

- Sun samu shiga wurin karfe 8:15 inda suka sace miji da mata tare da wani ma'aikacin

- Sai dai a halin yanzu, mazan biyu sun tsere inda suka bar matar auren a hannun miyagun

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kutsa kwatas din ma'aikatan filin jirgin sama na Jos dake yankin Heipang a jihar Filato inda suka sace matar aure.

An gano cewa 'yan bindigan sun samu shiga kwatas din wurin karfe 8:15 na dare kuma sun fara harbe-harbe babu kakkautawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wata majiya ta sanar da cewa an sace mutane uku da suka hada da matar aure tare da mijinta.

Amma mijin da dayan ma'aikacin sun samu hanyar kubuta daga hannun 'yan bindigan inda suka bar matar auren kadai a hannunsu.

KU KARANTA: Bidiyon liyafar biki ana kwashe kudin liki da babban bokiti ya janyo cece-kuce

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kwatas na ma'aikatan filin jirgi, sun sace matar aure. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Karin bayani na nan tafe...

KU KARANTA: Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje

A wani labari na daban, tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, a ranar Alhamis ya shiga ganawar sirri da Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun a ofishinsa dake Oke-Mosan, Abeukuta, babban birnin jihar.

Bankole ya isa ofishin gwamnan wurin karfe 4:25 na yamma kuma ya samu tarba ta musamman daga gwamnan.

Premium times ta ruwaito cewa, su biyun sun shiga ganawar sirri wanda har a halin yanzu ba a san abinda suka tattauna ba.

Source: Legit

Online view pixel