Mun fitar da N288bn kudin tallafin Korona, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Mun fitar da N288bn kudin tallafin Korona, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

- Mambobin Kwamitin karfafa tattalin arzikin Najeriya sun zauna ranar Alhamis

- Mambobin sun hada da Ministar Kudi da Ministar walwala da jin dadin al'umma

- Hakazalika akwai Ministan noma, ministan kwadago, ministan ayyuka, da karamin ministan kudi

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta bayyana cewa an fitar da kudi bilyan 288 cikin bilyan 500 da aka tanada don bada tallafi ga jama'a sakamakon illar da cutar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin.

Gwamnatin tace wannan kudi da ta saki sun taimaka wajen ceton ayyuka da samar da sabbin ayyuka milyan 2.1 yayinda aka kaddamar da sabbin hanyoyi na sama da kilomita 4000.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu akande, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki mai taken "Adadin sabbin ayyukan da aka samar da wadanda aka ceta ya zarce milyan 2 yayinda gwamnati ta saki kudin tallafin Korona N288bn."

Akande ya ce hakan ya bayyana ne bayan zaman kwamitin karfafa tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a fadar Aso Villa ranar Alhamis.

KU KARANTA: Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

Mun fitar da N288bn kudin tallafin Korona, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo
Mun fitar da N288bn kudin tallafin Korona, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo Hoto: @akandeoj
Source: Twitter

DUBA NAN: Kotu ta yankewa barayin waya hukuncin kisa a jihar Ondo

Wani sashen jawabin yace, "Ministoci da shugabannin ma'aikatun dake aiwatar da ayyukan shirin karfafa tattalin arziki sun bada rahoton nasarar da ake samu wajen aiwatar da shirin."

"Kawo yanzu an saki sama da rabin kudin da aka tanada don karfafa tattalin arzikin."

"Karkashin tallafin Survival Fund, an ceci ayyukan mutane 1.3m, hakazalika an samar da sabbin ayyuka 774,000 daga shirin PWP. Bugu da kari an samar da ayyuka 26,021 daga ayyukan gine-gine da gyare-gyare."

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin ayyukan yi cikin matasan Karkara ya zama babban kalubalen da ke rura wutan matsalar tsaro a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin karban bakuncin kungiyar masu sarrafa taki a Najeriya (FEPSAN), rahoton DailyTrust.

Shugaban kasan yace shekara da shekaru gwamnatocin da suka shude sun mayar da hankulansu kan raya birane maimakon raya Karkara.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel