Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari

Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana daya daga cikin abubuwan da ke rura wutan matsalar tsaro

- Buhari ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimakawa mutan Karkara

- Buhari ya karbi bakuncin yan kasuwan taki a fadarsa dake Villa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin ayyukan yi cikin matasan Karkara ya zama babban kalubalen da ke rura wutan matsalar tsaro a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin karban bakuncin kungiyar masu sarrafa taki a Najeriya (FEPSAN), rahoton DailyTrust.

Shugaban kasan yace shekara da shekaru gwamnatocin da suka shude sun mayar da hankulansu kan raya birane maimakon raya Karkara.

"A tsawon shekaru hudu da suka gabata, mun yi aiki tukuru domin daidaita abubuwa ta hanyar inganta aikin noma da bayar da kudade domin samar da ayyukan yi a Karkara," Buhari yace.

"Yayinda muke kokarin fadada yunkurin tabbatar da tsaro da dakile matsalar tsaro, ya nada muhimmanci in bayyana cewa ba za'a samu dawwamammen zaman lafiya da cigaba ba sai mun hada kai wajen samar da aikin yi ga mutan karkara."

"Saboda haka ina kira ga gwamnoni, bankuna, da masu sanya hannun jari su rika shiga Karkara," Buhari ya kara

KU KARANTA: Kotu ta jefa Baturen zabe kurkukun shekara 3 kan yiwa APC magudin zabe

Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari
Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari Credit: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Wata bakuwar cuta ta bulla jihar Sokoto, ta kashe dalibi 1, ta kwantar da 30

A bangare guda, Iyayen Leah Sharibu, ɗalibar da 'yan Boko Haram suka sace a makarantar Dapchi a watan Fabrairu 2018, sun bayyana rashin kwato ta da shugaba Buhari ya yi da 'Abun kunya'.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa iyayen sun yi wannan magana ne bayan rahoton da suka samu cewa Leah Sharibu ta sake haihuwa a karo na biyu.

A wani saƙo da ya fitar a madadin iyayen ta, Dr Gloria Puldu, yace iyayen Leah Sharibu na roƙon gwamnatin Najeriya ta amince da taimakon ƙasar Amurka wajen ceto ɗiyar tasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel