Kotu ta yankewa barayin waya hukuncin kisa a jihar Ondo

Kotu ta yankewa barayin waya hukuncin kisa a jihar Ondo

- Bayan shekaru shida, kotu ta yanke hukunci kan barayi uku a jihar Ondo

- Yan fashin sun shiga unguwa inda suka kwace wayoyi kuma suka tafi da babur

- Yanzu Alkali ya ce hukumar ta kashesu ta hanyar rataya

An yankewa 'yan uwa biyu, Sunday da Lucky Isaac, da wani dan babur, Ovie Nana, hukuncin kisa a ranar Juma'a kan laifin fashi da makami a jihar Ondo.

Alkali Yemi Fasanmi na babban kotun jihar ya tabbatar da laifi kan mutanen uku bayan kimanin shekaru shida ana Shari'a.

A ranar 11 ga Disamba, 2013, Sunday, Lucky da Ovie sun yiwa mazauna unguwar Bolorunduro fashi da makami inda suka kwashe dukiyoyi.

Masu laifin uku sun hada baki ne domin sace waya, kudi da wasu dukiyoyin mutanen.

Bayan damkesu a 2014, an gurfanar da su a kotu kan laifuka biyar.

A shari'ar da Alkalin ya yanke, ya bayyana cewa lallai ya gamsu da hujjojin da aka gabatar kan masu laifin kuma ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

KU KARANTA: Wata bakuwar cuta ta bulla jihar Sokoto, ta kashe dalibi 1, ta kwantar da 30

Kotu ta yankewa barayin waya hukuncin kisa a jihar Ondo
Kotu ta yankewa barayin waya hukuncin kisa a jihar Ondo
Source: Twitter

DUBA NAN:An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa

A bangare guda, wata babbar kotu dake jihar Akwa Ibom ta yankewa wani Farfesan jami'ar UNICAL, Peter Ogban, hukuncin daurin shekaru 3 a gidan gyara hali bayan kama shi da laifin sauya sakamakon zabe.

Ogban ya kasance baturen zabe a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom North-West a 2019

An tuhumeshi da laifin sanar da sakamakon zaben karya a kananan hukumomi biyu - Oruk Anam and Etim Ekpo.

Source: Legit

Online view pixel