An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa

An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa

- Iyayen Leah Sharibu sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya matukar basu kunya da ya gaza kubutar da diyarsu

- Leah Sharibu dai na cikin daliban da Boko Haram suka sace a shekarar 2018 amma har yanzun gwamnati bata kubutar da ita ba

- Rahoto ya bayyana cewa Leah Sharibu ta kara haihuwa a karo na biyu a hannun wadan da ke rike da ita

Iyayen Leah Sharibu, ɗalibar da 'yan Boko Haram suka sace a makarantar Dapchi a watan Fabrairu 2018, sun bayyana rashin kwato ta da shugaba Buhari ya yi da 'Abun kunya'.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa iyayen sun yi wannan magana ne bayan rahoton da suka samu cewa Leah Sharibu ta sake haihuwa a karo na biyu.

KARANTA ANAN: Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i

A wani saƙo da ya fitar a madadin iyayen ta, Dr Gloria Puldu, yace iyayen Leah Sharibu na roƙon gwamnatin Najeriya ta amince da taimakon ƙasar Amurka wajen ceto ɗiyar tasu.

Jawabin iyayen yace:

"Safiyar ranar 23 ga watan Maris ya zama wata mummunar rana garemu, saboda mun tashi da jita-jitar da ta ƙona mana rai cewa yar mu, Leah Sharibu, wacce har yanzun take hannun 'yan Boko Haram tsawon shekara uku ta haihu a karo na biyu."

"Wannan babban abun kunya ne ga janar Buhari da gwamnatinsa. Ya mance da wannan yarinyar a hannun 'yan ta'adda."

"Sati biyu da suka gabata, Nathan da Rabecca sun kirayi shugaba Buhari ya yi amfani da masu tattaunawa da yan bindigar da gwamnatinsa ke amfani dasu, waɗanda suka samu nasarar tattaunawa har aka saki dukkan ɗalibai musulmai 300 da aka sace a ƙanƙara a watan Disamba kwana shida kacal da sace su," a cewar iyayen.

An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa
An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

"A watan Fabrairu, sun sake samun nasarar tattaunawa da yan bindiga har aka kuɓutar da ɗaliban makarantar Kagara jihar Neja da kuma na jangeɓe jihar Zamfara duk a cikin kwanaki ƙalilan."

"Najeriya ta faɗi a kan Leah Sharibu. Wannan babban abin kunya ne, kasashen duniya suna daraja yan ƙasar su kuma zasu iya yin komai don kuɓutar da al'ummar su. Amma gwamnatin Buhari ta manta da Leah Sharibu na tsawon shekara uku."

"Ita ce dai gwamnatin data manta da ragowar 'yan matan Chibok 117 na tsawon shekara bakwai," inji iyayen.

KARANTA ANAN: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

Iyayen Leah na kira ga gwamnatin Janar Buhari da ta amince da taimakon Amurka don ƙuɓutar da ɗiyar su.

Musamman idan wakilan dake tattaunawa da yan bindigan gwamnatinsa suka kasa kuɓutar da ita kamar yadda suka kuɓutar da wasu ɗalibai kwanan nan.

Mayaƙan boko haram sun sace Leah sharibu tare da ɗalibai 109 (yan shekaru 11-19) daga makarantar sakandiren mata ta gwamnati dake Dapchi a ranar 19 ga watan Fabrairu, 2018.

Biyar daga cikinsu sun rasa rayukansu lokacin da aka tafi dasu. A ranar 21 ga Maris aka saki ɗalibai 104 bayan biyan kuɗin fansa.

Amma masu garkuwan sun riƙe Leah Sharibu saboda taƙi amince wa tabar addinin ta na kiristanci.

A wani labari kuma Tinubu ya tsallake mutanen da gobara ta shafa a Legas da Oyo, amma ya baiwa na Katsina N50m: Omokri

Omokri ya yi Alla-wadai da Tinubu kan yadda ya tsallake mutanen da gobara ta lashe dukiyansu a kasuwannin kudu maso yamma amma ya baiwa na Katsina gudunmuwar N50m.

Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina ranar Laraba don jajantawa mutanen da gobara ya shafa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel