Yanzu-yanzu: Kotu ta jefa Baturen zabe kurkukun shekara 3 kan yiwa APC magudin zabe
- Kotu ta yanke hukunci kan Baturen zabe da akayiwa zargin magudi a 2019
- An yi takkadama a 2019 kan zaben kujerar sanata tsakanin Apkabio da Ekpeyong
- INEC ta shigar da mutumin da ta dauka aiki kotu
Wata babbar kotu dake jihar Akwa Ibom ta yankewa wani Farfesan jami'ar UNICAL, Peter Ogban, hukuncin daurin shekaru 3 a gidan gyara hali bayan kama shi da laifin sauya sakamakon zabe, rahoton Daily Trust.
Ogban ya kasance baturen zabe a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom North-West a 2019
An tuhumeshi da laifin sanar da sakamakon zaben karya a kananan hukumomi biyu - Oruk Anam da Etim Ekpo.
Hukumar INEC da kanta ta shigar da shi kotu.
Kotun ta kama shi da laifin sauya sakamakon zabe don baiwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) nasara don kayar da Peoples Democratic Party (PDP).
Gabanin yanke hukuncin, Ogban ya bayyanawa kotu yadda aka sauya sakamakon don APC ta lashe zaben.
Ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio, ne dan takarar APC a zaben.
Yayinda tsohon mataimakin gwamnan jihar, Chris Ekpeyyong ne dan takarar PDP.
Akpabio ya sha kashi a zaben.
DUBA NAN: Ka nemi sulhu da 'yan bindigar nan tun kafin su kashe 'ya'yan mu, Iyayen Ɗalibai ga El-Rufa'i
KU DUBA: An dai ji kunya, Iyayen Leah Sharibu sun caccaki Shugaba Buhari da gwamnatinsa
A bangare guda, darektan yada labarai da wayar da kai na kungiyar Northern Elders’ Forum, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki gwamnatin APC mai-ci kan batun tsaro.
Dr Hakeem Baba-Ahmed ya na ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gaza kawo zaman lafiya tun da ya hau mulki.
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin nan na Arise TV a ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng