Labari Da Duminsa: Buhari Ya Gana Ga Gwamnan Benue, Samuel Ortom

Labari Da Duminsa: Buhari Ya Gana Ga Gwamnan Benue, Samuel Ortom

- Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya yi ganawar sirri da Shugaba Buhari a Aso Rock Abuja

- Ortom ya ce ya ziyarci shugaban kasar ne domin yi masa godiya saboda Allah wadai da ya yi da harin da aka kai masa

- Gwamnan na Benue ya kuma mika godiyarsa ga takwarorinsa gwamnoni bisa goyon bayan da suke bashi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya gana da gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, The Cable ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan wasu da ake zargin yan bindiga makiyaya ne suka kai wa gwamnan hari a ranar Asabar a lokacin da ziyarci gonarsa.

Labari Da Duminsa: Buhari Ya Gana Ga Gwamnan Benue Samuel Ortom
Labari Da Duminsa: Buhari Ya Gana Ga Gwamnan Benue Samuel Ortom. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Source: UGC

Gwamnan ya ce yan bindigan da adadinsu ya kai 15 sun rika binsa har zuwa gabar rafin da gonarsa ya ke sannan suka bude masa wuta tare da masu tsaronsa.

DUBA WANNAN: Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

Ortom ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre.

Da ya ke magana da manema labarai bayan ganawa da Shugaban kasa, Ortom ya ce ya ziyarci Buhari ne don yaba masa kan Allah wadai da ya yi da harin.

Ya ce Buhari ya amince da shawarwarin da ya bada kan batun tsaro a jihar.

Gwamnan ya ce ya yi bakin cikin ganin wasu na shakkun cewa yan bindiga sun kai wa tawagarsa hari, inda ya ce 'ko menene riban da zai samu kan karya game da abinda bai faru ba'.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An Kama Masuntar Ƙabilar Jukun 3 Kan Zargin Kaiwa Ortom Hari

Ya yi kira ga yan Najeriya su dena saka siyasa kan batun tsaro. Ya kuma yaba wa takwarorinsa gwamnoni da suka goyi bayansa.

Gwamnan ya ce bai laifi ya yi ba domin ya yi dokar da za ta amfani jiharsa.

Mutane da dama suna cigaba da tsokaci kan harin mafi yawancinsu na Allah wadai da shi.

Shugaba Muhammad Buhari kansa ya ce ba za a amince da irin wannan harin ba yayin da ya yi tir da maharan.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Online view pixel