'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da 'Yan Fashi 17 a Sokoto

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da 'Yan Fashi 17 a Sokoto

- Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta ce ta kama wadanda ake zargi da laifi su 17

- Wadanda aka kama akwai yan bindiga, masu garkuwa da mutane da yan leken asirinsu

- Kwamishinan yan sandan jihar Sokoto, Kamaldeen Okunlola ne ya ce za a gurfanarsu da su idan an gama bincike

Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da 'Yan Fashi 17 a Sokoto
'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da 'Yan Fashi 17 a Sokoto. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

"Yan garin sun taru sun bi sahun yan bindigan suka ceto wadanda aka sace suka kama Wanto, ya amsa cewa ya hada baki da wani Dari Digyal da Umaru Laka da a yanzu ake nemansu," in ji shi.

Shugaban yan sanda ya kuma ce rundunar ta kama wani Abubakar Altine da Dogo Buzu kan hadin baki, fashi da makami da garkuwa da mutane a kauyen Saketa da ke karamar hukumar Bodinga.

Ya ce yan sanda sun kwato makamai tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

KU KARANTA: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

"Rundunar ta kuma kama wani Abubakar Yusuf, wanda ya yi barazanar zai kashe wani Shamsu Goronyo idan bai bashi kudi ba ko kuma ya sace wani daga gidansu.

"An kuma kama wani Abdullahi Mode, wanda aka ce ya yi wa yan bindiga jagora sun kai hari a karamar hukumar Tangaza sun yi wa wani duka sun kwace masa N500,000.

"Rundunar ta kuma kama Umaru Buda da Bello Bameri kan harin da yan bindiga suka kai kauyen Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah inda mazauna kauyen da yan sanda suka fatattaki yan bindiga suka kashe uku suka kwato AK-47 da harsasai hudu," in ji shi.

Okunlola ya kara da cewa yan sandan sun kama wasu yan kungiyar masu kwacen waya da suka kwace a kalla wayoyi 24 yayin bikin Maulidi a jihar.

Kwamishinan yan sandan ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike a kansu.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel