Yanzu-Yanzu: An Kama Masuntar Ƙabilar Jukun 3 Kan Zargin Kaiwa Ortom Hari

Yanzu-Yanzu: An Kama Masuntar Ƙabilar Jukun 3 Kan Zargin Kaiwa Ortom Hari

- Rundunan yan sandan jihar Benue ta ce ta kama mutum 3 kan zargin kai wa Gwamna Ortom hari

- Yan sandan sun ce mutane ukun da aka kama masunta ne yan kabilar jukun da aka gani kusa da inda aka kai harin

- Rundunar ta ce a halin yanzu an tsare mutanen ana musu tambayoyi da nufin zurfafa bincike

Rundunar yan sanda ta kama masunta yan kabilar jukun su uku kan zargin hannu cikin harin da aka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a hanyar Tyo Mu a Makurdi, The Nation ruwaito.

Mai bawa gwamnan shawara kan tsaro, Kwanel Paul Hemba, ya tabbatar da hakan yayin da ya ke zagayawa da manema labarai wurin da aka kai harin a ranar Talata.

DUBA WANNAN: Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

Yanzu-Yanzu: An Kama Masuntar Ƙabilar Jukun 3 Kan Zargin Kaiwa Ortom Hari
Yanzu-Yanzu: An Kama Masuntar Ƙabilar Jukun 3 Kan Zargin Kaiwa Ortom Hari. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

Hemba ya ce yan sandan sun ga masuntar kusa da wurin da aka kai harin kuma ana bincike a kansu.

KU KARANTA: Jerin Ƙasashen Duniya Goma Mafi Hatsari a Shekarar 2021

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel