Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

- Hukumar tace fina-finai na jihar Kano ta kama, Bashir Dandago, mai wakokin yabon Annabi (SAW)

- Hukumar ta ce ta kama shi saboda fitar da wata wako inda ya zagi malaman Kano a kaikaice kan batun Sheikh Abduljabbar

- Ismail Na'abba Afakallah, shugaban hukumar tace fina-finan ya ce laifin Dandago shine fitar da wakar ba tare da izini ba

- Afakallah ya ce za a gurfanar da Dandago a gaban kotun Majistare da ke Nomansland a ranar Laraba

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

DUBA WANNAN: Mutum 19 Sun Rasu, 34 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Dandago: An Kama Mai Wakokin Yabon Annabi A Kano Saboda Fitar da Waka Ba Tare da Izini ba
Dandago: An Kama Mai Wakokin Yabon Annabi A Kano Saboda Fitar da Waka Ba Tare da Izini ba. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

A cewarsa, "Ya fitar da wata wakar inda ya ke zagin mutane a kaikaice, wadda hakan na iya tada fitina a tsakanin mutane.

"Laifinsa a gaban hukumar shine fitar da waka ba tare da neman sahalewar ta ba.

"Ba za mu kyalle mutane su rika rayuwa ba tare da tsari ba.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC Ta Bawa Ambode Sabon Muƙami

"Za mu kai shi kotu domin a gurfanar da shi, kuma kotu ne za ta fadi irin hukuncin da ya dace a yi masa," Afakallah ya kara da cewa.

Za a gurfanar da Dandago a gaban alkalin kotun Majistare da ke Nomanslanda a Kano a ranar Laraba.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164