Gwamnonin Arewa sun fadi abin da ya sa ‘Yan bindiga su ka nemi ran Ortom, abin da za ayi

Gwamnonin Arewa sun fadi abin da ya sa ‘Yan bindiga su ka nemi ran Ortom, abin da za ayi

- Kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da abin da ya faru da Samuel Ortom

- Gwamnonin Arewa sun ce ‘Yan bindiga su na neman tada rikici a Benuwai da ko ina

- Simon Lalong ya yi kira a zage-dantse, ya bukaci hukumomi su yi cikakken bincike

A ranar Lahadi, 21 ga watan Maris, 2021, kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya, ta yi magana game da harin da aka kai wa Samuel Ortom na jihar Benuwai.

Jaridar The Cable ta ce gwamnan Filato wanda shi ne shugaban gwamnonin jihohin Arewa, ya bayyana harin da aka kai wa abokin aikin na su abin damu wa.

Gwamna Simon Bako Lalong ya kuma yi kira ga jama'a su gudanar da bincike a kan lamarin.

KU KARANTA: A shirya sabon yaki a Najeriya idan Gwamnati ta kashe Ortom - Wike

Darektan yada labarai da hulda da ‘yan jarida na gwamnan na Filato, Makut Macham, ya fitar da jawabi, ya na tir da harin da aka kai wa tawagar Samuel Ortom.

Jawabin da Makut Macham ya fitar da ranar Lahadi da yamma, yake cewa an kai wa gwamnan hari ne saboda a jawo rudani a jihar Benuwai da fadin kasar nan.

Kungiyar ta bukaci duk wasu jami’an tsaro da su ke da alhaki su yi cikakken bincike domin bankado wadanda su ka kai harin da duk masu daure masu gindi.

A jawabin, Simon Lalong ya jinjina wa dakarun da ke tsare abokin aikinsa game da kokarin da su ka yi wajen tsare ran gwamnan da kuma ragowar ‘yan tawagarsa.

KU KARANTA: Tsageru sun kamfanonin kasar waje su fita, su bar Neja-Delta

Gwamnonin Arewa sun fadi abin da ya sa ‘Yan bindiga su ka nemi ran Ortom, abin da za ayi
Gwamnonin yankin Arewa Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Shugaban kungiyar ta gwmanonin Arewa ya ce ya zama dole a tashi-tsaye a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ya dabaibaye Najeriya a halin da ake ciki.

Gwamnan ya ce kungiyarsu za ta cigaba da ba jami’an tsaro hadin-kai domin su tsare yankin Arewa.

Kungiyar Arewa Youth Federation ta ce sam babu wata hujjar kusa ko nesa da ke nuna an kai wa Samuel Ortom hari kamar yadda ya fito ya fada wa jama'a.

Duk da ikirarin da wasu Fulani su ka yi, kungiyar Arewa Youth Federation ta ce ita ba ta yarda makiyaya Fulani ne su ka kai wa Gwamnan Benuwai hari ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel