Wike ya ce a shirya sabon yaki, a kai Najeriya makabarta idan Gwamnati ta kashe Ortom

Wike ya ce a shirya sabon yaki, a kai Najeriya makabarta idan Gwamnati ta kashe Ortom

- Nyesom Wike ya soki harin da aka kai wa tawagar gwamna Samuel Ortom

- Gwamnan ya ce Gwamnatin tarayya za a kama idan Samuel Ortom ya mutu

- Wike ya ce idan aka yi nasarar kashe Ortom, to yaki zai barke a kasar nan

Mai girma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya tofa albarkacin bakinsa a game da harin da ‘yan bindiga su ka kai wa gwamna Samuel Ortom.

Gwamnan na jihar Ribas ya ce gwamnatin tarayya za a damke da laifi idan har aka kashe abokin aikinsa, kuma takwaransa watau gwamnan jihar Benuwai.

Daily Trust ta rahoto Nyesom Wike ya na cewa sabon yakin basasa ya na jiran kasar nan idan gwamna Samuel Ortom ya mutu a hannun ‘yan bindiga.

KU KARANTA: Ba zan bar PDP, in koma APC mai fama da cutar daji ba - Wike

“Idan ku ka kashe Ortom, ku yi shirin birne Najeriya.” Jaridar ta rahoto gwamna Wike ya na fadan wannan a garin Fatakwal, jihar Ribas a ranar Lahadi.

Gwaman Wike ya ce: “Idan wani abu ya faru da gwamna Ortom, gwamnatin tarayya za a samu da laifi, kuma ta shirya sai ya zama babu Najeriya a tarihi.”

Nyesom Wike ya yi tir da yadda ake kai wa gwamnonin jihohi hari kuru-kuru yanzu a kasar nan.

Gwamnan na PDP ya yi ikirarin a lokacin zaben 2019, babban jami’in sojan kasa, Janar Jamil Sarham da wasu manyan kusoshin APC sun nemi su hallaka shi.

KU KARANTA: Makiyaya suka kai mani hari - Gwamna Ortom

Amma babu wata hujja da gwamna Wike ya bada da za ta gamsar da cewa Manjo Janar Jamil Sarham ko wasu jiga-jigan APC sun yi yunkurin kashe shi a 2019.

‘Yan bindiga sun kai wa tawagar Ortom hari ne a titin Makurdi/Gboko a karamar hukumar, Makurdi.

A baya kun ji cewa Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da miyagun 'yan bindiga suka kai wa Gwamna Samuel Ortom.

Shugaban kasar ya kuma gargadi 'yan siyasa su daina amfani da harin domin cimma manufofinsu na siyasa, ya yi kira a binciki abin da ya auku.

Garba Shehu ya bayyana wannan a sanarwar da fitar a madadin Shugaban Kasa a ranar Lahadi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel