Wata sabuwa: Tsagerun Neja-Delta su na neman su fatattaki kamfanonin da ke aikin hako fetur

Wata sabuwa: Tsagerun Neja-Delta su na neman su fatattaki kamfanonin da ke aikin hako fetur

- ‘Yan Unyekisong Akwa Ibom su na yi wa kamfanoni barazana a Neja-Delta

- Kungiyar tsagerun Unyekisong Akwa Ibom sun ce kamfanonin mai su tashi

- Unyekisong Akwa Ibom tace kamfanonin mai su kan jawo masu matsaloli

Wasu tsageru su na neman kawo wa gwamnatin tarayya barazana bayan sun umarci kamfanonin kasar waje su bar yankin kasar mai arzikin mai.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa wasu tsageru a karkashin lemar Unyekisong Akwa Ibom, sun bukaci kamfanonin ketare su fice daga Akwa Ibom.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugabannin kungiyar tsagerun Unyekisong Akwa Ibom; Janar Dede Udofia da Manjo Ibanga Ekang a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Wike: A kama Gwamnatin Buhari da laifi idan aka kashe Ortom

Dede Udofia da Ibanga Ekang sun fitar da jawabi ne a garin Uyo, su ka ce sun ba kungiyoyin kasashen wajen gajeren lokaci su gaggauta barin fadin yankin.

Rahoton ya ce Unyekisong Akwa Ibom gamayya ce tsagerun da ke tada-kafar baya a Akwa Ibom.

Kungiyoyin da su ka hadu a wannan tafiya sun hada da: Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND), the Niger Delta Volunteer Force, da Movement for the Actualisation of the Niger Delta Republic.

Haka zalika kungiyoyin Niger Delta People’s Salvation Force, Niger Delta Avengers, Niger Delta Liberation Force da Niger Delta Movement for Justice da Niger Delta Warriors, su na tare da su.

Tsagerun Neja-Delta su na neman su fatattaki kamfanonin da ke aikin hako fetur
Tsagerun Neja-Delta Hoto: www.bbc.com/news/world-africa-36953269
Asali: UGC

KU KARANTA: Idan ba a cika mana sharudodi ba, za mu balle daga kasar nan – NINAS

Unyekisong Akwa Ibom ta ce kamfanoni da su ke aikin hako danyen mai a yankin sun hana al’umma sakat.

Kungiyar Unyekisong Akwa Ibom ta ke cewa kamfanonin ketaren sun hana mutanen Neja-Delta neman na abinci, sannan sun lalata masu rayuwa da aikin na su.

Wasu 'yan ta'addan Neja-Delta da suka ajiye bindigogi sama da shekaru biyar, sun sake yin fito-na-fito inda suka yi barazanar kai hari a garuruwan Legas da Abuja.

Tsagerun sun zargi gwamnatin tarayya da watsi da yankinsu, da tura sojoji su kashe mutane.

A cewar wani tsageran da ya rufe fuskarsa, tun bayan amince wa da yarjejeniyar afuwar, har yau, babu makarantu, asibiti, ruwa da titunan da aka gina masu a yankin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel