Wani Matashi Ya Gamu Da Ajalinsa Cikin Ruwa a Jihar Kano
- An gano gawar wani mutum cikin ruwa a kauyen Garin Bature da ke Jihar Kano
- Alhaji Saminu Yusuf, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya sanar da hakan
- Saminu Yusuf ya ce jamiansu sun ciro gawar sun mika ga wakilin dagacin ƙauye kuma an fara bincike
Wani mutum mai shekaru 25, Anas Abdulsalam ya riga mu gidan gaskiya yayin da ya shiga ruwa a ƙauyen Garin Bature a ƙaramar hukumar Bichi.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Alhaji Saminu Yusuf kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya sanar.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara
"Jami'in dan sanda mai suna Yahuza Mohammed ya kira mu misalin ƙarfe 2.05 na rana kan neman kai ɗauki.
"Bayan kiran da aka mana, mun tura tawagar mu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru domin ciro gawar daga ruwa.
"Mun mika gawar Abdulsalam ga wakilin mai dagajin ƙauyen Gidan Bature Sha'aibu Isma'il," ya ce cikin sanarwar da ya fitar.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho
Kakakin hukumar ya ce ana bincike kan abinda ya yi sanadin rasuwar mutumin.
Ya gargadi iyaye su rika hana yaransu zuwa wanka a tafki ko rafi.
A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.
Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.
Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng