Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho

Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho

- An kama wasu mutane da ake zargin Fulani ne da kai hari gidan mahaifiyar Sunday Igboho

- Olayomi Koiki, mai magana da yawun Sunday Igboho, ne ya sanar da hakan a dandalin sada zumunta

- Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama shima ya ce ya yi magana da Sunday Igboho ya tabbatar da lamarin

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari gidan mahaifiyar mai rajjin kare hakkin yarabawa, Cif Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, ya tabbatar da hakan a daren ranar Lahadi ta shafinsa na Twitter.

DUBA WANNAN: Hotunan Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho
Yanzu-Yanzu: An Kai Hari Gidan Mahaifiyar Sunday Igboho. @TheNationNews
Asali: Twitter

Ya rubuta: "Wasu mutane uku Fulani sun kai hari gidan mahaifiyar Chief Sunday Adeyemo da ke Igboho misalin karfe 7.54 na yamma.

"Biyu cikinsu sun tsere, daya yana hannu an tsare shi a ofishin yan sanda da ke Igboho."

Tsohon ministan sufuri, Femi Fani Kayode ya tabbatar da labarin harin a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal

Ya ce: "Yan ta'adda uku aka kama a gidan mahaifiyar Sunday Igboho ba biyu ba. An kama daya biyu sun tsere.

"Yanzu na gama magana da Sunday Igboho kuma ya fada min cewa an kama yan ta'adda Fulani yan kasar waje a gidan mahaifiyarsa da ke Igboho jihar Oyo a daren yau.

"Nufinsu shine su kai wa Mama hari. Daga cikinsu daya ya tsere yayin da dayan na hannun yan sanda. Wadanda suka turo su suna wasa da wuta."

Tsohon ministan ya kara da kira ga wadanda ke nufin kai wa Igboho hari su sauya mugunyar tunaninsu domin hakan ba zai haifar wa kasar da mai ido ba.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel