Ba Tabbas Zamu Yi Rigakafin COVID19 Saboda Babu Cutar A Jihar Mu, Inji 'Yan Majalisun Kogi

Ba Tabbas Zamu Yi Rigakafin COVID19 Saboda Babu Cutar A Jihar Mu, Inji 'Yan Majalisun Kogi

- Yan majalisar tarayya wadan da suka fito daga jihar Kogi sub bayyana cewa basu da tabbas ko zasu yi allurar rigakafin COVID19

- A cewar shugaban 'yan majlisun da suka fito daga jihar, Smart Adeyemi, suna goyon bayan gwamnan jihar su Yahaya Bello kan cewa babu cutar a jihar su

- A ranar Talata ne aka yi ma shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan rigakafin kuma ya bawa sauran sanatoci sati biyu kowa ayi masa

Sanatoci da 'yan majisar wakilai da suka fito daga jihar Kogi sun bayyana cewa har yanzun basu yanke zasu yi allurar rigakafin korona ko ba zasu yi ba.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya yi tashi alllurar ranar Talata data gabata kuma ya ba sauran sanatoci sati biyu suje su yi rigakafin, jaridar Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamnati ta ce ba za ta tilastawa 'yan Najeriya yin rigakafin Korona ba

Sai dai, a lokacin da yake magana da manema labari a madadin 'yan uwansa, shugaban 'yan majalisun da suka fito daga jihar Kogi, Smart Adeyemi, yace 'yan majalisun tarayya nan da suka fito daga Kogi basu yanke hukunci akan lamarin rigakafin har yanzun.

Adeyemi, wanda shine mataimakin shugaban sanatocin da suka fito daga Arewa, yace dukkan 'yan majalisun tarayya 12 daga jihar ta Kogi na goyon bayan gwamnan jihar, Alhaji Yahaya Bello, wanda ya bayyana cewa babu cutar a jihar sa.

Ya ce abu ɗaya da ka iya sawa su yi rigakafin shine don kada idan sun yi tafiya zuwa wani wuri su ɗakko cutar su kawo ma jihar tasu.

A cewar Adeyemi: "Yan majalisun da suka fito daga jihar Kogi basu yanke hukuncin ko zasu yi allurar rigakafin korona ba, idan ma zasu yi sai dai don suna Abuja kuma akwai cutar anan, amma babu COVID19 a jihar Kogi."

Ya kuma gargaɗi mutanen dake zargin gwamnan kogi don ya bayyana cutar bata kama kowa ba a jihar sa.

Ba Tabbas Zamu Yi Rigakafin COVID19 Saboda Babu Cutar A Jihar Mu, Inji 'Yan Majalisun Kogi
Ba Tabbas Zamu Yi Rigakafin COVID19 Saboda Babu Cutar A Jihar Mu, Inji 'Yan Majalisun Kogi Hoto: @officialGYBKogi
Source: Twitter

"Bansan irin baiwar da Allah ya yiwa jihar Kogi ba, saboda cutar bata kashe mutanen mu. Idan cutar na kashe mutanen mu, ina ganin zan zama mutum naa farko da zai ƙalubalanci gwamnan mu, amma cutar bata kashe mutanen mu, kai babu cutar ma a jihar," injishi.

KARANTA ANAN: Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal

"Na yarda da gwamnan mu cewa babu cutar a jihar Kogi domin idan akwai ta data rinƙa kashe mutane. Ya bayyana cewa cutar na tsoron jihar Kogi kuma mun yarda da gwamnan mu don yasan abun da yake yi," a cewar Adeyemi.

Ya ƙara da cewa ma'aikatar lafiya ta ƙasar nan ta faɗa masa cewa basu san meyasa cutar bata kashe mutanen jihar Kogi ba.

"Bazai yuwu mu kashe mutanen mu kawai saboda muna san tabbatar ma mutane cewa cutar gaskiya ce, bawai mun yarda da gwamnan mu hakanan bane, a'a mun yarda ne saboda babu wanda cutar ta kashe a jihar," Adeyemi ya faɗa.

Sanatan ya ƙara da cewa gwamna Yahaya Bello mutum ne mai ƙarfin guiwa, yana yanke hukunci ne da zaran ya gano ainihin abinda ke faruwa a cikin al'ummarsa da kuma abinda suke so.

Sanata Adeyemi ya ce babu wanda zai nuna ma jihar Kogi ƙauna sama da ɗan asalin jihar, kamar Gwamnan da kuma 'yan majalisun jihar.

A wani labarin kuma Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma

Shugaban na NDLEA ya samar da kididdiga game da yawan ta’ammali miyagun kwayoyi a yankuna da dama na Najeriya

Marwa na da kwarin gwiwar cewa rashin tsaro a kasar zai ragu idan aka duba lamarin shan miyagun kwayoyi.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel