Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma

Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma

- Buba Marwa, shugaban hukumar NDLEA ya nuna damuwa kan yadda ake shan miyagun kwayoyi a kasar

- Shugaban na NDLEA ya samar da kididdiga game da yawan ta’ammali miyagun kwayoyi a yankuna da dama na Najeriya

- Marwa na da kwarin gwiwar cewa rashin tsaro a kasar zai ragu idan aka duba lamarin shan miyagun kwayoyi

Buba Marwa, shugaban hukumar hana fatauci da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ya bayyana cewa a yanzu haka yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ya na cikin wadanda suka fi shan miyagun kwayoyi a kasar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 19 ga Maris, 2021, a Ogbomoso, jihar Oyo yayin bikin bude cibiyar gyara masu ta'ammali da miyagun kwayoyi da wata kungiya da aka sani da Ogbomoso First Initiative ta gina.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban na NDLEA ya bayyana cewa akwai alaka tsakanin shan kwayoyi da karuwar aikata laifuka a Najeriya.

Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma
Shugaban NDLEA, Marwa ya ce ta'ammali da miyagun kwayoyi ya fi kamari a Kudu maso Yamma Hoto: @THISDAYLIVE
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: APC tana da cutar Kansa, ba zan taba sauya sheka zuwa jam'iyyar ba, Wike ya bayyana

A cewarsa, yawan yadda ake amfani da miyagun kwayoyi a kasar na a kamar haka:

1. Kudu maso yamma - 22.4%

2. Kudu maso kudu - 16.6%

3. Kudu maso gabas - 13.8%

4. Arewa maso gabas - 13.6%

5. Arewa ta tsakiya - 10%

Ya ce:

“Muna fuskantar kalubalen shan kwayoyi a Najeriya amma kalubale ne da za a iya magance shi. Don cimma wannan, dole ne duk masu ruwa da tsaki su haɗu don magance matsalar. Kalubalen kwayoyi ba ya nuna bambanci tsakanin Kiristoci da Musulmai. Babu wata al'umma da wannan matsalar ba ta shafa ba."

Ya yi nuni da cewa ta’addanci, tayar da kayar baya, satar mutane, da sauran ayyukan ta’addanci duk suna da asali daga amfani da miyagun kwayoyi.

Marwa ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro za ta ci gaba da kasancewa idan ba a duba shan miyagun kwayoyi ba a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2023: Ba zan goyi bayan Jonathan ba idan ya tsaya takara a APC, in ji Wike

A cewar Sahara Reporters, ya bukaci gwamnoni su gina akalla cibiyoyin gyara mutane uku a jihohinsu, yana mai cewa ya kamata kowane mazaba ya kasance yana da guda daya.

Ya kuma ƙarfafa wa sarakunan gargajiya, cibiyoyin addini da makarantu gwiwar yin yaƙi da shan ƙwaya a tsakanin matasa.

A baya mun ji cewa birgediya-Janar Buba Marwa ya yi kira da a gudanar da gwajin shan kwayoyi ga dalibai da ‘yan siyasa, musamman wadanda ke takarar ofisoshin gwamnati a kasar, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Marwa, wanda shi ne Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a wata ganawa da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a Marina.

Ya yaba wa kokarin da gwamnatin jihar ta yi a kan batun shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin Jihar, yana mai bayyana Lagos a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta sanya wasu hanyoyi na zamani don yakar matsalar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit

Online view pixel