Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal

Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal

- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ce jam'iyyar APC na daf da rushewa a Nigeria

- Tambuwal ya ce hakan zai faru ne saboda irin matsalolin da suka dabaibaye jam'iyyar a matakin jihohi da kasa

- Gwamnan na Sokoto ya yi wannan jawabin ne yayin taron kaddamar da yakin neman zabe na PDP gabanin zaben kananan hukumomi a jihar

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a ranar Asabar ya ce jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na daf da rushewa, rahoton Daily Trust.

Ya yi wannan hasashen ne yayin kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, gabanin zaben kananan hukumomi da za a gudanar a jihar.

Jam'iyyar APC ta kusa rushewa, in ji Gwamna Aminu Tambuwal
Jam'iyyar APC ta kusa rushewa, in ji Gwamna Aminu Tambuwal. Hoto: @daily_trust
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Saraki Ya Roki Ƴan Nigeria Su Sake Bawa PDP Dama a 2023

Jam'iyyar APC ta ce ba za ta shiga zaben ba saboda wasu matsaloli da ta gani a cewar ta.

Sai dai gwamnan ya ce jam'iyyar ta APC ta janye daga zaben ne saboda tana fama da matsalolinta a jihar da ma kasa baki daya.

Gwamnan ya kara da cewa jam'iyyar ta APC ba ta da wani abinda za ta nuna na cigaba tun da ta hau mulki a 2015.

KU KARANTA: Ku Shirya Birne Nigeria idan Ku Ka Kashe Ortom: Wike Ya Gargaɗi FG

"Matsaloli sun yi wa jam'iyyar yawa kuma ta kusa rushewa," in ji shi.

An yi bikin kaddamarwar ne a Gwadabawa, daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da hare-haren yan bindiga a jihar.

Amma gwamnan ya yi kira ga jama'a su bawa jami'an tsaro hadin kai a kokarinsu na dawo da zaman lafiya.

Tambuwal, wanda ya ce gwamnatinsa na yin ayyuka lunguna da sako na jihar ya bukaci jama'a su rika kulawa da kayayyakin gwamnati.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel