Coronavirus: An raba rigakafi a Abuja da Jihohin Najeriya 35 ban da jihar Kogi

Coronavirus: An raba rigakafi a Abuja da Jihohin Najeriya 35 ban da jihar Kogi

- Hukumar NPHCDA ta ce an kai alluran AstraZeneca zuwa kowace Jiha

- Jihar da ta fi bare wajen yin rigakafin annobar Coronavirus ita ce Kogi

- Gwamnan Kogi bai bada dama ayi tanadin allurar COVID-19 a jiharsa ba

A ranar Alhamis ne Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta raba magungunan cutar COVID-19 a jihohi 35 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa jihar Kogi ce kurum ba ta samu wadannan magunguna ba.

Shugaban hukumar NPHCDA mai kula da dakunan shan magani na kasa, Dr. Faisal Shuaib ya sanar da wannan a ranar 18 ga watan Maris, 2021.

Faisal Shuaib ya ce ba a ba jihar Kogi AstraZeneca ba ne saboda wasu dalilai, daga ciki akwai rashin dakuna masu sanyi da za a adana maganin.

KU KARANTA: COVID-19: Yahaya Bello ya kori tawagar NCDC daga Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ba ta gyara dakunan adana magungunan ba ne saboda rashin gamsuwar ta game da rigakafin da ainihin annobar Coronavirus.

Shugaban NPHCDA ya yi duk wannan bayanai ne bayan wani zaman majalisar tattalin arziki na NEC wanda aka yi a Abuja kamar yadda aka saba yi.

Darektan hukumar kiwon lafiyan ya bayyana cewa su na bukatar isassun tsaro saboda maganin tsagera da za su iya kawo hari, su jawo asarar magungunan.

Dr. Shuaib ya ke cewa kwamitin yaki da COVID-19 ya nemi hadin-kan hukumar ICPC domin ganin an raba magungunan na AstraZeneca yadda ya dace.

Coronavirus: An raba rigakafi a Abuja da Jihohin Najeriya 35 ban da jihar Kogi
Yahaya Bello Hoto: legit.ng

KU KARANTA: Gwamnan Kogi, Bello bai dauke da kwayar COVID-19 - Hadiminsa

Shuaib ya ce za a karo wa Najeriya wasu sahu na magungunan daga kasar waje nan da wani lokaci.

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya tsaya tsayin-daka a kan ba za ayi wa mutanensa allurar rigakafin ba, ya ce ba cutar COVID-19 ke gabansu ba.

Kwanaki kun ji cewa dole kungiyar gwamnoni na kasa ta fito ta yi martani yayin da Yahaya Bello ya ce kashe mutane ake so ayi da rigakafin cutar COVID-19.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan na jihar Kogi ya fada wa taron jama'a cewa su yi watsi da rigakafin da aka bijiro da shi, ya ce shirin kashe mutane ne.

Dr. Kayode Fayemi da NGF sun yi kokarin magance shakkun da ke zukatan jama'a game da rigakafin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit Nigeria

Online view pixel