Kogi: Gwamna Bello bai dauke da kwayar COVID-19 Inji Hadiminsa
Mai girma gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello bai kamu da cutar Coronavirus ba kamar yadda jama’a su ke ta yadawa a cikin ‘yan kwanakin nan.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Onogwu Muhammed. Jawabin ya zo ne a tsakiyar makon nan.
“Gwamna, da Iyalinsa da Danginsa da kuma Mukarrabansa ba su nuna wata alama na kamuwa da cutar COVID-19 ba, duk su na cikin koshin lafiya.”
Sakataren yada labaran ya fayyace wannan lamari ne yayin da jama’a su ke yada jita-jitar cewa gwamnan ya kamu da cutar COVID-19 da ta ke yawo.
Mista Onogwu Muhammed ya kara da cewa: “(Gwamna) Bello ya yi kira ga mutanen jihar su kauracewa shiga jama’a, su kuma rike tsabtan jikinsu.”
KU KARANTA: Gwaji: COVID-19 ta kama Hadimin Shugaban kasa Abba Kyari
Sakataren yada labaran na gwamnatin Jihar Kogi ya tabbatar da cewa rade-radin da ake yi na cewa gwajin asibiti ya nuna Bello ya kamu da cutar COVID-19.
“Gwamnan ya yi wa wadanda su ke dauke da cutar COVID-19 fatan samun waraka daga Allah Madaukaki cikin gaggawa, ba tare da kakkautawa ba.”
A wani gajeren bidiyo da ke yawo, an ji gwamnan ya na cewa: “Ba ni da COVID, masu yi mani fatan COVID za su kamu da HIV, ina nan lafiya lau garau.”
A game da annobar COVID-19, Sanatan Osun ta tsakiya, Ajibola Basiru da wasu manyan Alkalai biyar a jihar sun killace kansu a Osun domin gudun yada cutar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng