Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona

Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona

- Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi martani ga ikirarin Gwamna Yahaya Bello mara tushe kan rigakafin COVID-19

- Gwamnan na jihar Kogi ya fada ma taron jama'a da su yi watsi da rigakafin, inda yayi ikirarin cewa an shirya rigakafin ne don kashe mutane

- Sai dai, NGF ta fada ma gwamnan cewa COVID-19 gaskiya ce kuma yana da matukar muhimmanci ayi wa yan Najeriya rigakafin cutar

Yayinda yan Najeriya ke tsammanin sakamakon ganawar gwamnonin jihohi 36 kan rabon rigakafin korona, sakataren kungiyar gwamnonin Najeriya ya fada ma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, cewa annobar gaskiya ce kuma dole a dauki mataki.

Darakta Janar na kungiyar, Mista Ashishana Okauru, ya fada ma jaridar Thisday cewa gwamnoni na duba yiwuwar amfani da dabaru daban-daban don wayar da kan jama’a kan rigakafin.

Shugaban kungiyar, Dr. Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya bayyana a makon da ya gabata cewa babban damuwar gwamnonin a halin yanzu shine magance shakkun da ke zukatan yan Najeriya game da rigakafin.

Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona
Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Ya ce a lokacin taron gwamnonin na karshe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun sanar da Shugaban kasar cewa akwai bukatar wayarwa da al’umma kai kan yadda za a magance hauhawan hatsarin annobar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta gabatar da shaida a shari’arta da Babachir David Lawal a Kotu

A cewar Fayemi: “Mun fada ma Shugaban kasar cewa akwai bukatar a sako sarakunan gargajiya, shugabannin addini da bangaren nishadantarwa da sauransu domin wayar da kai da kuma jadadda muhimmancin rigakafin.”

Bello, wanda yayi watsi da manufar COVID-19 da karyata wanzuwar cutar a jiharsa, ya fada ma taron jama’a da kada su yarda da rigakafin cutar saboda an yi su ne don kashe su.

A cewar gwmnan na jihar Kogi: “An kirkiri rigakafi cikin kasa da shekara daya da bayyanar korona. Har yanzu babu rigakafin HIV, zazzabin cizon sauro, kansa, ciwon kai da sauran cututtukan da ke kashe mu. Suna so suyi amfani da rigakafin korona wajen kawo cutar da za ta kashe ku da mu. Allah ya kiyaye.”

Amma Okauru ya ce Shugaban kungiyar gwamnonin ya jadadda cewa cutar gaskiya ce don haka yan Najeriya sun cancanci rigakafin.

Ya lissafo gwamnonin da suka kamu da cutar a baya wadanda suka hada da Mista Seyi Makinde na Oyo, Sanata Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma Malam Nasir el-Rufai na jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya

Sauran sune Dave Umahi na jihar Ebonyi, Dr. Okezie Ikpeazu na jihar Abia, Sanata Ifeanyi Okowa na jihar Delta, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

A gefe guda, wata kungiya mai rajin kare martabar jam'iyyar APC ta soki gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, akan kalamansa da ke sukar rigakafin allurar kwayar cutar korona.

A cewar kungiyar (APC Mandate Defenders) Kalaman gwamna Yahaya Bello daidai suke da tunzura jama'a domin tozarta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda TheNews ta wallafa.

Kungiyar ta bayyana cewa hankalinta ya kai kan wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo inda aka ji Gwamnan na fadawa magoya bayansa kar su yarda da rigakafin saboda tana kisa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel