COVID-19: Gwamna Yahaya Bello ya yi martanin da ya kori tawagar FG daga jiharsa

COVID-19: Gwamna Yahaya Bello ya yi martanin da ya kori tawagar FG daga jiharsa

A ranar Alhamis ne gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bukaci wakilan NCDC da ma'aikatar lafiya da suka sauka a jiharsa da su killace kansu na kwanaki 14 ko su bar jihar a take.

Gwamnatin tarayya ta tura wakilai jihar Kogi don su taimaka wa jihar da gwajin cutar coronavirus.

Kamar yadda jaridar The Cable ta bayyana, jihohin Kogi da Cross River ne kadai ba a samu mai cutar ba a fadin Najeriya.

A makon da ya gabata, Chikwe Ihekweazu, darakta janar na NCDC ya nuna rashin gamsuwarsa da samfur din da aka karba daga jihohin. Ya ce akwai bukatar kara yawan samfur din.

Amma kuma jihohin Kogi da Cross River sun zargi cibiyar da yunkurin kai musu cutar har gida.

Bayan kungiyar ta isa gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Lokoja, Bello ya ce dole ne a bi dokokin kungiyar kiwon lafiya ta duniya.

WHO ta bukaci a killace duk matafiyi na kwanaki 14 inda daga nan a yi mishi gwajin cutar.

KU KARANTA: COVID-19: Yadda aka tilasta wa limamai share gidan hakimi a Kano

Noah Andrew, shugaban wakilan gwamnatin tarayyar ya mika wasika ga gwamnan inda ya yi mishi bayanin abinda jami'an kiwon lafiya suka sauka yi a jihar.

Ya ce sun isa ne don kai kayayyakin aiki kamar yadda suka yi a sauran jihohin kasar nan.

Ya ce za a bar mutum biyu daga cikin 'yan kungiyar don taimakawa jihar.

"Mun zo taimaka wa jihar ne wajen duba samfur tare da tabbatar da shirinta na ko ta kwana," yace.

A yayin jawabin Bello bayan karbar wasikar, ya bayyana mayakan da jihar ta dauka wajen yaki da annobar.

Ya ce jihar na da matukar gogewa wajen yaki da cututtuka masu yaduwa wadanda suka hada da zazzabin Lassa da na Malaria. Ya ce wadannan gogewar ne ake amfani da su a wannan halin.

Ya bukaci jami'an NCDC da a gwada su tare da killacesu a cibiyar killacewa ta jihar ko kuma su kama gabansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel