Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Samar Da Sukari Na Ƙasa

Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Samar Da Sukari Na Ƙasa

- Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya naɗa Mr Adedeji Zacch a matsayin shugaban hukumar samar da suga na ƙasa

- Sanarwar nadin ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey

- Adedeji Zacch kwararrre ne a bangaren kudi da kasuwanci kuma ya taba riƙe muƙamin kwamishinan kudi a jihar Oyo

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mr Adedeji Zacch a matsayin babban sakataren Hukumar Samar Da Sukari Na Ƙasa na wa'adin shekaru hudu na farko, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan watsa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey, cikin sanarwar da ya fitar ya ce nadin ya yi daidai da sashi na 5(1) na dokar hukumar samar da sukari ta kasa (1993).

Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Samar Da Sukari Na Ƙasa
Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Samar Da Sukari Na Ƙasa. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

Ya ce nadin zai fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Maris na 2021.

A cewar sanarwar, "Mr Adedeji na da digiri na farko da na biyu a bangaren aikin akanta daga jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife da kuma satifiket a bangaren tattalin arziki daga Harvard Kennedy School of Government da ke Amurka kuma kwararrren akanta ne da ya shafe shekaru 15 yana aiki.

KU KARANTA: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

"Kafin nadinsa, ya yi aiki a kamfanin Procter and Gamble da ke Legas sannan ya rike mukamin kwamishinan kudi a jihar Oyo daga 2011-2015," a cewar sanarwar.

"Shugaban ƙasa yana kira ga wanda aka yi wa naɗin ya yi wa kasar sa hidima cikin aminci da gaskiya yayin gudanar da ayyukansa."

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel