Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

- Yan sanda a jihar Kano sun yi karin bayani game da bakin da suka shigo jihar da rakuma

- Wasu mutanen Kano suna fargabar bakin sun iso jihar ne da wata mummunar maufa

- Amma binciken da yan sanda ta yi ya nuna yan kasuwa ne kuma ba su dauke da wani mugun abu

- Rundunar yan sandan ta kuma ce mutanen za su sayar da kayansu ne su yi siyaya a kasuwar Dawanau su koma gida cikin kwanaki 20

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan raƙuma da suka ɓulla a Kano
Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan raƙuma da suka ɓulla a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Bakin sun yada zango a Rimin Zakara da Dorayi a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.

Mr Haruna, mataimakin sufritanda yan sanda ya ce sun yi bincike tare da hukumar kula da shige da fice (Immigration) sun gano cewar bakin na dauke da takardun izinin shigowa kasar.

"Ba mu same su da wani abu mai alaka da laifi ba. Bincike ya nuna dillalan kanwa ne daga Jamhuriyar Nijar kuma suna da takardun shigowa kasar.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido

"Mun gayyaci shugabanninsu domin tambayoyi, kuma mun tuntubi ofishin jakadancin Nijar kan batun.

"Binciken da muka kara yi ya nuna cewa ba za su wuce kwanaki 20 inda suka sayar da hajarsu sannan suka siya kayan abinci a kasuwar Dawanau domin komawa gida Damagaram," ya kara da cewa.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel